Mene ne takunkuman CAATSA kuma ta yaya cire su da Amurka za ta yi zai amfani Turkiyya?
DUNIYA
4 minti karatu
Mene ne takunkuman CAATSA kuma ta yaya cire su da Amurka za ta yi zai amfani Turkiyya?Cire takunkuman Amurka zai yi amfani sosai ga Turkiyya a fannonin tattalin arziki da fasahar ƙere-ƙere, in ji masu nazari.
Shugaba Erdogan ya marabci Shugaban Amurka Donald Trump a Ankara a ranar 7 ga Yuli don halartar taron NATO.. / Reuters / Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya faɗa a ranar Talata cewa zai ɗage takunkumin CAATSA da ya ƙaƙaba wa Turkiyya.

"Za mu cire takunkumin. Lokaci ya yi da za mu yi hakan... ba ma son a hukunta abokanmu. Abu ne mai sauƙi," in ji Trump ga manema labarai kafin tattaunawa ta sirri da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a Ankara gabanin babban taron NATO na 2026.

Dokar Kare Hakkokin Amurka Ta Hanyar Takunkumi (CAATSA) doka ce ta Amurka ta 2017 da aka tsara don dakatar da muhimman mu'amaloli da sassan tsaro da leƙen asiri na Rasha.

A watan Disambar 2020, Amurka ta sanya wa Turkiyya takunkumi a ƙarƙashin CAATSA saboda sayen tsarin tsaron sararin samaniya na Rasha S-400.

Waɗanne takunkumai ne?

Dole ne a lura da cewa takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Turkiyya bai taɓa shafar tattalin arziki ko rundunar sojinta ba.

Madadin haka, waɗannan takunkuman sun shafi Hukumar Masana'antun Tsaro ta Turkiyya (SSB) - wata hukumar gwamnati da ke da alhakin kula da masana'antar tsaro ta ƙasar, sayen fasahar soji, da kuma zamanantar da rundunar sojojin Turkiyya - tare da wasu manyan jami'ai.

Takunkumin ya kuma haifar da hana lasisin fitar da kaya na Amurka da bayar da izini ga hukumar.

Haka nan, waɗannan takunkuman sun taƙaita wa cibiyoyin kuɗi na Amurka bai wa hukumar lamuni ko bashi fiye da dala miliyan 10 a cikin kowane wata 12.

Sun kuma haɗa da hana tallafin Bankin Fitarwa da Shigo da Kaya na Amurka don fitar da kaya zuwa ga hukumar ta Turkiyya.

Sun buƙaci hukumomin Amurka su ƙi amincewa da lamuni daga cibiyoyin kuɗi na duniya waɗanda za su iya amfanar hukumar.

An kuma sanya takunkumin tafiye-tafiye zuwa Amurka ga jami'an da aka ambata.

Sannan a wani bangare na matakan an kuma cire Turkiyya daga mallakar jirgin yaki samfurin F-35.

Turkiyya ta ci gaba da nanata cewa sayen garkuwar makamai masu linzami ta S-400 daga daga Rasha wani mataki ne na karfafa tsaronta ta sama.

Jami'an Turkiyya sun yi Allah wadai da takunkumin a matsayin rashin adalci da kuma hari a fili kan ikon mallakar kasa, suna masu lura da cewa wani bangare na matsin lamba ne maimakon damuwar tsaro ta gaske.

Ba abin mamaki ba ne, idan aka ce takunkumin ya kara hanzarta yunkurin Turkiyya na ci gaba da bunkasa masana'antar tsaronta.

Tare da kamfanoni sama da 500 da ke aiki a fannin tsaro da jiragen sama da kuma jiragen sama marasa matuki na duniya da suka riga suka fara samarwa, Ankara ta mayar da kalubalen zuwa wata dama ta rage dogaro da kamfnonin waje don bukatun kayan aikin soji.

Ta yaya cire takunkuman zai taimaka wa Ankara?

Masu sharhi sun ce dage wadannan takunkuman zai samar da fa'idoji masu yawa ga Turkiyya a fannin dabarun cigaba, tattalin arziki, da fasaha.

Na farko, zai ba da damar sake shigar da Turkiyya cikin shirin samar da F-35.

Kin amincewar Amurka shi ne cewa amfani da Turkiyya za ta yi da garkuwar makamai masu linzami kirar Rasha samfurin S-400 zai sanya jiragen yakin Amurka cikin hatsari, wanda hakan zai sa su kasa dacewa da tsarin NATO.

Duk da haka, Turkiyya ta dage cewa babu wani rikici tsakanin tsarin biyu, yayin da take gabatar da kwamiti don yin nazarin batun.

Dage takunkumin zai ba Ankara damar samun wadannan jiragen yaki masu ci gaba, wanda zai taimaka wajen sabunta rundunar sojin saman Turkiyya da karfi irin na zamanin yau.

Na biyu, cire takunkuman kan hukumar masana’antun tsaron Turkiyya zai bude sabbin hanyoyi don hadin gwiwar tsaro tsakanin Ankara da Amurka.

Turkiyya za ta sake samun damar samun lasisin fitar da kaya daga Amurka da tallafin kudi. Wannan zai sauƙaƙa ƙarin sayayya na soji, canja wurin fasaha, da ayyukan haɗin gwiwa.

Na uku, kawo ƙarshen takunkumin CAATSA zai kawar da babban abin da ke tayar da hankali a dangantakar Amurka da Turkiyya, wanda zai share fagen zurfafa hadin gwiwa.

Bugu da ƙari, kawo ƙarshen rikicin ba iya Turkiyya zai ƙarfafa ba, har ma da NATO daki ɗaya.