Rundunar ‘yansanda ta gano wani wajen ƙera bindigogi ba bisa ƙa’ida ba a ƙaramar hukumar Potiskum a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Nijeriya tare da kama mutum bakwai da ake zargi da ƙera bindiga.
Rundunar ta ce an kama waɗanda ake zargin ne a wata maƙera da ke Tashar Adua a kan hanyar Danchuwa a garin Potiskum ranar litinin.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Dungus Abdulkarim ya fitar ta bayyana hakan.
“Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta cim ma wata gaggarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙar laifuka a fadin jihar,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar ta ce jami’an rundunar a yankin Potiskum tare da haɗin gwiwar ‘yansanda daga hedikwatar ‘yansanda ta yankin, sun ƙaddamar da wani samame bisa bayanan sirri game da zargin ƙera bindigogi ba bisa ƙa’ida ba a yankin.
Abdulkarim ya ce an kama waɗanda ake zargi yayin da aka kwashe abubuwa daga maƙerarar a matsayin shaida.
Abubuwan da aka ƙwacen sun haɗa da ƙananan bindigogi biyu da bututun bakin bindiga 24, da gindin bindiga tara da bindigogi baka da ba sa aiki huɗu, da na’urar goge ƙarfe da kuma adda ɗaya .
“An gudanar da samamen ne bayan an sami bayanan sirri masu ƙwari game ayyukan wasu maƙera da ke ƙera bindigogi ba bisa ƙa’ida ba,” a cewar Abdulkarim .














