Ghana na karɓar baƙuncin wani taron duniya a ranar Alhamis inda ake neman sauya goyon baya ga neman biyan diyyar cinikin bayi a siyasance zuwa wani alƙawari na adalci a aikace.
Taron, wanda ya haɗo shugabanni daga sassan Afirka da ƙasashen Karebiyan, na zuwa ne bayan Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ƙudirin da ya ayyana cinikin bayi da aka yi ta Tekun Atalantika a matsayin "mafi munin laifi kan bil’adama."
Tun lokacin da aka amince da ƙudirin a watan Maris, fafutukar neman diyya ta samu "irin ƙarfin da bai taɓa samu ba," kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Ghana Samuel Ablakwa ya bayyana.
Yayin da ya kasance wani abin da bai zama dole a bi shi ba, ƙudirin – wanda Shugaban ƙasar Ghana John Mahama ya ɗauki nauyinsa – ya zarce batun kawai a yarda cewa lamarin ya faru, ya nemi ƙasashe da suke da hannu a cinikin bayin su biya diyya.
'Za mu yi nasara a yaƙin neman biyan diyya na adalci'
"Mun yi nasara a yaƙi kan bauta, mun yi nasara a yaƙi kan mulkin mallaka, mun yi nasara a kan mulkin wariyar launin fata, kuma muna da ƙwarin gwiwa cewa za mu yi nasara a kan rashin adalci na rashin biyan diyya," kamar yadda Ablakwa ya shaida wa taron.
Amincewa da ƙudirin da MƊD ta yi ya nuna goyon baya mafi ƙarfi da ƙasashen duniya suka yi wa lamarin biyan diyya, inda ya samu goyon bayan ƙasashe 123 na MƊD .
A da ana yi mata kallon cibiyar cinikin bayi ta tekun Atalantika, a halin yanzu Ghana "tana sauyawa daga kasancewa wajen aikata laifi zuwa wata mafaka ta samun sauƙi da adalci ta biyan diyya", kamar yadda Ablakwa ya shaida wa ɗaruruwan mahalarta taron.
Ƙasar ta Yammacin Afirka ta kasance a gaba-gaba wajen haɗa mutanen da ba a Afika suka zaune ba, inda ta ba da shaidar zama ɗanƙasa ta Ghana ga fiye da mutum 1,000 a cikin ‘yan shekarunnan.
Hanyoyin samun adalcin diyya
Mahama ya ayyana kafa kwamiti uku domin duba hanyoyin samun adalcin biyan diyya.
Ɗaya zai kasance kwamiti mai ba da shawara a ƙarƙashin shugabannin ƙasashe, da kwamitin ƙwararru da zai mayar da hankali kan biyan diyya, sai kuma wani na ukun da zai duba batutuwa na shari’a da ke da alaƙa da biyan diyyar.
"Tambayar da ke a gabanmu a yanzu ba wai kan ko za a iya sauya tarihi ba ne – ba za a iya sauya shi ba – ko muna da ƙarfin zuciyar fuskantarsa cikin gaskiya da kuma jajircewa ta yadda za mu sauya amincewar zuwa mataki mai ma’ana," kamar yadda Mahama ya bayyana.
Jerin masu jawabi a taron na kwanaki uku ya haɗa da shugabannin ƙasashen Barbados da Saliyo da Senegal da Namibia da Laberiya.
Ɗaya daga cikin mahalarta taron Mariam Abdoulaye, daga ƙasar Burkina Faso, ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa Afirka na tsammanin diyya a nau’in "tsararrun kuɗin diyya ga gwamnatoci da al’ummomi" daga tsoffin ƙasashen da suka yi mulkin mallaka ko kuma cibiyoyi da ke da alaƙa da cinikin bayi, tare da soke bashi ko kuma sake tsara bashi da kuma mayar da kayayyakin tarihi da aka sace.













