| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Hukumar leƙen asiri ta Turkiyya ta kama babban jagoran Daesh tare da dawo da shi ƙasar
Wanda ake zargin ne ke jagorantar ayyukan watsa labarai na kungiyar ‘yan ta’addar bayan kama wanda ya gabace shi, in ji jami’an tsaro.
Hukumar leƙen asiri ta Turkiyya ta kama babban jagoran Daesh tare da dawo da shi ƙasar
MIT ta ce Kazanci ya tafi daga Turkiyya zuwa yankin iyalar Afganistan-Pakistan / AA

Hukumar Leken Asiri ta Kasa ta Turkiyya, ko MIT ta kama wani babban jami’in kungiyar ta’addanci ta Daesh tare da dawo da shi zuwa Turkiyya, in ji jami’an tsaro a ranar Laraba.

Farmakin da aka kai ya nufi rashen watsa labarai na Daesh-K, reshen kungiyar ta’addar na Afganistan, in ji majyoyin.

Dan ta’addar da aka bayyana sunansa da Ahmet Kazanci kuma aka fi ani da “Abu Ubeyde” da “Abu Ibrahim”. ya shiga hannu a lokacin farmakin.

Majiyoyin tsaro sun ce Kazanci ne ya kama ragamar kula da ayyukan watsa labarai a Turkiyya bayan kama wanda ya gabace shi Ozgur Altun.

MIT ta ce Kazanci ya tafi daga Turkiyya zuwa yankin iyalar Afganistan-Pakistan, ya shiga kungiyar ta’adda ta Daesh-K tare da taka rawa a sansaninta, in ji majiyoyin.

Masu bincike sun gano cewa ya yi aiki tare da Altun wajen daukar mayaka daga Turkiyya zuwa yankin Afganistran-Pakistan kuma daga baya ya zama mai alhakin kula da ayyukan watsa labarai na kungiyar bayan kama Altun.

Majiyoyin sun ce bayanan sirri da MIT ta tattara sun yi nuni da cewa Kazanci ya tsira dage hare-hare ta sama da aka kai wa ‘yan ta’addar Daesh a Pakistan inda daga baya ya yi shirin sake shiga Turkiyya ba bisa ka’ida ba don ci gaba da ayyuka a madadin kungiyar.

Majiyoyin sun kuma ce daga baya sai aka kama shi a wani farmaki da aka kai a kusa da iyakar kasar.

A yayin tambayoyi, kazanci ya yi ikirarin alaka da Altun, ya bayyana irin horo da ya samu a kungiyar, sannan kuma ya dinga yi mata ayyukan watsa labarai da farfaganda.

Majiyoyin tsaro sun kuma tabbatar da cewa farmakin da aka kai ya lalata shirin ‘yanta’addar Daesh na kai wa Turkiyya hari tare da bankado hanyoyin da ake bi wajen daukar wa kungiyar ma’aikata.