Hukumomi a Afirka ta Kudu sun kama wani mutum mai shekara 28 bayan an gano kunamu 150 rayayyu masu dafi, waɗanda aka ɓoye cikin tufafinsa a filin jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa da ke Cape Town.
Hukumar ‘yansandan Afirka ta Kudu, (SAPS), ta ce an yi kamen ne ranar 12 ga Yuni a wani aiki da ɓangaren da ke yaƙi da safarar dabbobin masu fuskantar barazanar ƙarewa ya yi, bisa bayanan sirri da haɗin-gwiwar hukumar CapeNature mai kula da dabbobin daji.
Jami’ai sun gano wanda ake zargin ne ta hanyar amfani da kwatancen da aka ba su game da shi, kafin su kama shi su kuma bincika jakunkunansa.
Yayin binciken, hukumomi sun gano kunamu 150 masu dafi da ransu da ya ɓoye cikin tufafinsa. An kama wanda ake zargin bisa laifin riƙe namun daji ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ya saɓa wa dokokin kare halittu da muhalli.
Hukumomi ba su gano inda matafiyin zai tafi ba tukuna ko kuma kimar kunamun da aka ƙwace a hannunsa, waɗanda har yanzu ana nazari kansu. An miƙa dabbobin ga ƙwararru domin tabbatar da tsaronsu da kuma ganin sun samu kulawar da ta dace.
Lamarin ya sake nuna yawan fasaƙwaurin namun daji a Afirka ta Kudu, wanda kasuwanci ne da bai tsaya kan sanannun halittun irin su karkanda da giwaye kawai ba, har wasu halittu da ba a sansu sosai ba ciki har dangogin ƙadangare da dangogin gizo, a kasuwar bayan fage ta ƙasa-da-ƙasa.
Ana sa ran wanda ake zargin zai bayyana a gaban kotun majistire ta Bellvill, domin fuskantar tuhume-tuhumen da za a yi masa.







.jpeg?width=512&format=webp&quality=80)



