| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Nijar za ta karɓi tallafin dala miliyan 33 daga IMF
IMF ya ce tattalin arzikin Nijar ya ci gaba da kasancewa mai ƙarfi, inda ya bunƙasa da kashi 6.9 cikin 100 a shekarar 2025, kuma ana hasashen zai kai kashi 7 cikin 100 a shekarar 2026.
Nijar za ta karɓi tallafin dala miliyan 33 daga IMF
Idan aka samu amincewar, kuɗaɗen za su taimaka wajen biyan buƙatun kuɗaɗen waje na Nijar tare da tallafa wa sauye-sauyen da ake aiwatarwa. / Reuters

Niger na shirin karɓar sabon tallafi na kusan dala miliyan 33 daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya bayan cim ma yarjejeniya a matakin ma’aikata kan nazari na tara na shirin sauye-sauyen tattalin arzikinta ƙarƙashin shirin Extended Credit Facility (ECF).

An cim ma yarjejeniyar ne a yayin wata ziyarar tawagar IMF zuwa Yamai daga ranar 2 zuwa 12 ga Yuni.

Sai dai yarjejeniyar na bukatar amincewar Kwamitin Zartarwa na IMF, wanda ake sa ran zai yi nazarinta a ƙarshen watan Yuli.

Idan aka samu amincewar, kuɗaɗen za su taimaka wajen biyan buƙatun kuɗaɗen waje na Nijar tare da tallafa wa sauye-sauyen da ake aiwatarwa.

IMF ya ce tattalin arzikin Nijar ya ci gaba da kasancewa mai ƙarfi, inda ya bunƙasa da kashi 6.9 cikin 100 a shekarar 2025, kuma ana hasashen zai kai kashi 7 cikin 100 a shekarar 2026, musamman sakamakon ci gaban da aka samu a fannin noma da kuma haƙar albarkatun ƙasa.

Asusun ya kuma yaba wa yadda Nijar ta tafiyar da harkokin kuɗaɗenta, yana mai cewa gibin kasafin kuɗi ya ragu zuwa kashi 2.9 cikin 100 na ma’aunin GDP a shekarar 2025, sakamakon ƙaruwa a kuɗaɗen shiga na cikin gida da kuma yawan kuɗaɗen da ake samu daga fitar da man fetur.

Duk da ƙalubalen tsaro, sauyin yanayi da matsalolin samar da kuɗaɗe, IMF ya ce Nijar ta samu ci gaba wajen ƙarfafa harkokin kuɗaɗen gwamnati, biyan basussukan da ake bi bashi, da kuma inganta gaskiya da riƙon amana, ciki har da wallafa kwangilolin man fetur da aka kulla da kamfanonin mai.

Gwamnatin Nijar ta yi alƙawarin ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da za su ƙara kuɗaɗen shiga, ƙarfafa shugabanci nagari da kuma tallafa wa bunƙasar kamfanoni masu zaman kansu.