Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ba da damar kafa wani kwamiti na musamman na shirin yaƙi da cutar Ebola da sauran abubuwa masu fitowa da ke barazana ga lafiyar al’umma.
Shugaban ya kuma ba da umarnin fitar da kuɗi naira biliyan 10 nan take domin aikin shirin ko-ta-kwana.
Ana sa ran kuɗin zai ƙarfafa shirin aiki na Hukumar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) da kuma tallafa wa shirin ƙasar na iya ɗaukar matakan gaggawa a fannin lafiyar al’umma.
Wannan na cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya fitar a Abuja ranar Talata.
Kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa zai kasance ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, kuma zai haɗu da mambobi daga ma'aikatu da hukumomi masu alaƙa, tare da wakilai daga jihohi.
Damar da shugaban ƙasar ya bayar ta biyo bayan wani zaman da shugaban ma’aikatan ya yi da manyan masu ruwa da tsaki ne domin nazari kan shirIN Nijeriya da kuma samar da dabarun tunkarar yiwuwar shigar Ebola ƙasar.
Zaman ya samu halarcin wakilai daga ma’aikatar tsaron cikin gida da Hukumar Filayen Jiragen Saman Nijeriya (FAAN), da Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), da Hukumar Sufurin Jiragen Sama na Fararen Hula ta Nijeriya (NCAA) da sauran masu ruwa da tsaki.
Tinubu ya kuma umarci dukkan jihohi da ke da filayen jiragen saman na ƙasa da ƙasa da yankunan da ke da kan iyaka da wasu ƙasashe, da kuma hukumomi masu alaƙa, su miƙa shirye-shiryensu na ko-ta-kwana da buƙatu na kuɗi da kuma baƙatu na agaji domin aiwatar da su bai-ɗaya.
Shugaban ya kuma amince da wasu jerin matakai na ƙarfafa matakan sa ido da na kai ɗauki a fadin ƙasar.
Waɗannan sun haɗa da zurfafa bincike kan matafiya a filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa ta hanyar inganta gwajin zafin jiki da kuma tafiyar da mutane.
Sauran matakn sun haɗa da sa iso kan fasinjojin da ke shigowa ta kamfanonin jiragen ƙasashen da ake ganin suna cikin babbar barazana ciki har Air Uganda da RwandAir da Air Tanzania da TAAG Angola Airlines da Kenya Airways da kuma Ethiopian Airlines.
Kwamitin na musamman zai kuma tabbatar da fara aikin wuraren turawa da kuma killace mutane nan take a filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa a Legas da Abuja, da irin waɗannan wuraren da za a samar a sauran filayen jiragen sama.
Bugu da ƙari, za a fara aiki da manhajar QR code ta bayyana yanayin lafiyar fasinjoji da suke tahowa ta ƙasashen da ke fuskantar barazanar cutar kafin su shiga Nijeriya.
Gwamnatin ta kuma amince da a yi amfani da maganin kashe ƙwari domin kawar da ƙwayoyin cuta a filayen jiragen saman a matsayin matakan rigakafi.
Tinubu ya kuma bai wa kwamitin umarnin tuntuɓar hukumomin tsaro da na diflomasiyya da sufuri domin ƙayyade tashi da sauƙar jirage daga ƙasashen da ake ganin suna fama da barazanar fama da cutar.


.jpeg?width=720&format=webp&quality=80)


.jpeg?width=128&format=webp&quality=80)







