Isra’ila ta ƙaddamar da hare-haren sama kan yammaci da tsakiyar Iran yayin da aka ba da rahotannin fashewar abubuwa a wasu biranen Iran, kamar yadda kafafan watsa labaran Isra’ila da na Iran suka ruwaito.
Sojin Isra’ila ta yi iƙirarin cewa da sanyin safiyar ranar Litinin sojin samanta ta kai hari kan wurare na sojin “gwamnatin Iran.”
Gidan talabjin mallakar gwamnatin Iran ya ba da rahoton fashewar abubuwa a babban birnin ƙasar, da kuma a Tabriz da Isfahan, yayin da kamfanin dillancin labaran Tasnim ya ba da rahoton fashewar abubuwa kusa da birnin Karaj.
IRNA ya kuma ba da rahoton cewa an ji aƙalla fashewar abubuwa uku a Isfahan.
Hare-haren na zuwa ne sa’o’i bayan Iran ta ƙaddamar da wasu hare-haren makamai masu linzami zuwa arewacin Isra’ila biyo bayan harin saman Isra’ila kan babban birnin ƙasar Lebanon, a unguwannin da ke wajen kudancin birnin Beirut.
Isra’ila ta yi biris da Trump
Hare-haren sun kuma ƙara barazana ga yarjejeniysar tsagaita wuta da ta fara aiki ranar 8 ga watan Afrilu wadda ta shiga kwananta na 100, inda Amurka take ƙoƙarin cim ma wata yarjejeniya da Tehran domin kawo ƙarshen rikicin.
Trump ya kuma nemi ya shawo kan Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, yayin da Isra’ila ta zargi Tehran da tafka wani "mummuna kuskure".
"Zan kira ga Bibi yanzun nan kuma zan gaya masa kada ya rama ," kamar yadda ɗanjaridan Axios Barak Ravid ya ambato Trump yana cewa a wata hira ta wayar tarho, yana mai amfani da laƙabin Netanyahu.
"Isra’ila ta kai harinta kuma Iran ta kai harinta . Ba ma buƙatar wani kuma ," kamar yadda aka ambato Trump yana cewa.
Daga baya Ravid ya wallafa wani saƙo cewa wani jami’in Amurka ya ce Trump ya yi magana da Netanyahu, duk da cewa fadar White House da Trump ba su yi tsokaci ba tukunna.
Sakataren harkokin wajen Birtaniya Yvette Cooper na cikin masu kira da a kai zuciya nesa.
"Sake fara rikici tsakanin Iran da Isra’ila ba zai tamaki kowa ba," kamar yadda ta wallafa a shafinta na X, tana mai kira da a bi tafarkin diflomasiyya.
Fragabar yaƙi ta kama fatan tsagaita wuta
Tehran ta haƙiƙance cewa duk wata yarjejeniya ta kawo ƙarshen yaƙi gabaɗaya dole ya dakatar da rikicin dake faruwa a Lebanon, inda Isra’ila take kai hare-hare kan ƙungiyar Hezbollah da Iran ke mara wa baya, kuma ta yi gargadin cewa duk wani sabon jerin hare-hare kan Beirut zai tayar da "sake fara cikakken" yaƙe-yaƙe.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Ali Safari ya shaida wa gidan talabijin din Al-Mayadeen cewa hare-haren Tehran sun zo bayan makonni na kamewa kan tsangwama na Isra’ila , kamar yadda kafofin watsa labaran cikin gida suka ruwaito.
Rundunar kare juyin juya halin Iran mai ƙarfi ta bayyana harin a masatyin “gargaɗi” bayan Isra’ila ta kai hari kan unguwannin kewayen kudancin Beirut daga farkon ranar, tana mai barazanar ƙarin hare-hare idan aka maimaita hari mara sa dalili.
Sojin Isra’ila ta kuma bayyana ranar Litinin cewa tana aiki dokin kakkaɓo wani makami mai linzami da aka harbo daga Yemen, inda ‘yantawaye suka ƙaddamar da hare-hare kan Isra’ila.
Ranar Lahadi, ofishin Netanyahu ya fitar da sanarwar cewa sojin ƙasar ta "kai hari kan wata cibiyar ba da umarni na tsageru a gundumar Dahiyeh ta Beirut, a matsayin martani ga harin da Hezbollah ta kai kan ƙasar Isra’ila".
Samamen ya kashe mutum biyu da kuma raunata ƙarin 20 , kamar yadda ma’aikatar lafiyar Lebanon ta bayyana.
Tehran ta kuma dakatar da duk jiragen da ke shigowa filin jiragen samanta na ƙasa da ƙasa , kamar yadda kafafan watsa labaran cikin gida na ƙasar suka bayyana ranar Lahadi.
Ƙarin tashin hankalin ya tayar da farashin ɗanyen mai yayin da fatan sake buɗe mashigar ruwan Hormuz, muhimmiyar hanyar ruwa ta jigilar mai da gas , wadda Iran ta riga ta rufe, ya sake dishewa.
Hare-hare na bayan nan da Isra’ila ta kai kan Iran sun ƙara matsi kan ƙoƙarin cim ma tsagaita wuta na din-din-didn a yaƙin da ake tsakanin Iran da Amurka.
Sabon musayar wutan ya tayar da yiwuwar komawar yaƙi da ƙarfi da kuma dagula dukkan ƙoƙarin shiga tsakani domin kawo ƙarshen yaƙin.
















