Gasar wasanni mafi girma a duniya za ta fara ranar 11 ga Yuni, inda ƙungiyoyi 48 za su fafata don cin Kofin Duniya na FIFA 2026. Amma babbar tambayar ita ce, shin gwarazan ƙasashen Turai, ko gwarazan nahiyar Amurka ne za su ɗaga kofin.
Ga taƙaitaccen bayani game da tawagogin da suke da mafi kyawun damar lashe Gasar:
Sifaniya
Tun bayan nasararsu a 2010, tawagar Sifaniya ba ta samu cigaba mai nisa a gasar ba, kuma suna ta ƙoƙarin sake gina tawagarsu.
A gasar 2026, Sifaniya za ta zo da ‘yanwasa da yawa haziƙai, ciki har da Lamine Yamal Pedri (Pedro Gonzalez Lopez) na Barcelona, da Rodri (Rodrigo Hernandez Cascante) na Manchester City.
Sifaniya tana matsayi na biyu a jerin gwanayen ƙwallon ƙafa na FIFA, kuma masana da dama suna kallon su a matsayin ɗaya daga cikin masu iya lashe gasar bana.
Faransa
Akwai wata tsohuwar ta’ada game da Kofin Duniya na ƙwallon ƙafa, inda ake kiran sa da "ba ka son zakarun bara", saboda ba wai kawai zakarun bara suna gaza sake lashe kofin ba, sau da yawa ana fitar da su tun da wuri.
Zakaru huɗu a jere suna shan irin wannan kaye, wato Faransa (2002), Italiya (2010), Sifaniya (2014) da Jamus (2018).
Faransa ta karya wannan "baki" ta hanyar isa wasan ƙarshe na Gasar Duniya ta 2022, amma sai suka sha kashi a hannun Argentina, bayan sun yi nasara a 2018.
A wannan karon, tawagar Faransa cike take da ƙwararru da dama, ciki har da Michael Olise na Bayern Munich, Ousmane Dembele na PSG, Rayan Cherki na Manchester City, da Kylian Mbappe na Real Madrid.
Tawagar na kan matsayi na farko a jerin gwanayen kwallo na FIFA, kuma suna da babban buri na yin nisa a gasar.
Ingila
Ingila ta kasance mai ban mamaki dangane da tawagar ƙasar. Suna yawan samar da zaratan 'yanwasa masu ƙwarewa a tsawon lokaci. Bugu da ƙari suna da gasar da ake ganin ita ce mafi karfi a duniya, wato gasar Firimiya.
Duk da haka, ban da nasarar lashe gasar a 1966, tawagar ba ta cimma wani babban abu ba har zuwa yau.
A wannan kaka, tawagar mai suna Three Lions suna da zurfin zaɓin ‘yanwasa a tawagar, musamman ‘yan tsakiya da ‘yan gaba.
Ingila na a matsayi na huɗu a duniya, kuma wasu daga cikin fitattun ‘yanwasansu sun haɗa da Declan Rice na Arsenal, Jude Bellingham na Real Madrid, da Harry Kane na Bayern Munich.
Brazil
Brazil ita ce tawagar ƙwallon ƙafa mafi nasara a duniya, saboda tarihin lashe kofunan duniya biyar. Tawagar mai suna Selecao suna da wani tarihin da babu wata ƙungiyar da ta yi kamar shi.
Sun cancanci shiga kowace Gasar Duniya. Duk da haka, nasarar Brazil ta ƙarshe a gasar ta faru ne a 2002, kuma mafi nisan da suka kai tun daga baya shi ne zuwa samifainal a 2014, inda suka sha kaye da ci 7-1 a hannun Jamus.
A duniya Brazil na matsayi na shida, kuma tawagar na da taurari kamar Raphinha na Barcelona, da Vinicius Junior na Real Madrid. Har ila yau, suna ƙarƙashin jagorancin babban koci mai ƙima, Carlo Ancelotti, wanda ya maye gurbin Dorival Junior.
Argentina
Ko da yake Argentina ba su da irin tagomashi nasara kamar na 2022, lokacin da suka lashe Kofin Duniya, tawagar tasu dakakkiya ce a fagen fafatawa, kuma suna da ƙwarewa da gogewa da zai iya nuna barazana a gasar.
Wasu daga cikin ‘yanwasa masu fice sun haɗa da Lautaro Martinez na Inter Milan, Alexis Mac-Allister na Liverpool, Julian Alvarez na Manchester City, da Lionel Messi na Inter Miami. Argentina na a matsayi na uku a jerin FIFA, kuma ba za a ɗauke su da wasa ba.
Netherlands
Tawagar mai laƙabin Oranje, sau da yawa ana saka su cikin mafi kyau amma ba ta taɓa lashe Gasar Duniya ba. Netherlands ta kai wasan ƙarshe sau uku, a 1974, 1978 da 2010, amma tana shan kashi a dukansu.
Wataƙila ba su da manyan ‘yanwasa kamar na baya-bayan nan irin su Van Persie, Robben, ko Van Nistelrooy. Amma ƙwarewa da damar da suke da ita na iya kai su nesa a gasar.
Wasu daga cikin ‘yanwasansu sun haɗa da Virgil van Dijk na Liverpool, Stefan de Vrij na Inter Milan, Tijjani Reijnders na Manchester City, da Ryan Gravenberch na Liverpool. Netherlands suna a matsayi na bakwai a jerin FIFA.
Jamus
Wata babbar tawagar ƙwallo a duniya ita ce Jamus, wadda ake wa laƙabi da Die Mannschaft. Sun lashe Kofin Duniya a 2014, kuma yanzu tana da tawaga mai matasa masu ƙwarewa, don haka zai zama kuskure a yi watsi da su.
Tawagar Jamus ta haɗa da Joshua Kimmich na Bayern Munich, Florian Wirtz na Liverpool, Jamal Musiala na Bayern Munich da Leon Goretzka na Bayern Munich. A yanzu Jamus suna a matsayi na goma a jerin FIFA.
Portugal
Tare da zurfin zaɓin d suke da shi a kowane rukunin ‘yanwasa, tare da haɗakar masu gogewa da matasa masu baiwa, Portugal tana sahun tawagogi masu ƙarfin iya lashe gasar.
Za su zo da 'yanwasa kamar Nuno Mendes na PSG, Vitinha na PSG, Bruno Fernandes na Manchester United, da zaƙaƙurin ɗanwasan gaba, Cristiano Ronaldo na Al Nassr.
A duniya, Portugal suna a matsayi na biyar a jerin matsayi na FIFA, kuma suna neman lashe kofin Gasar Duniya a karo na farko a bana.








