Kasashen Turkiyya da Nijar sun rattaba hannu kan jerin yarjejeniyoyin haɗin gwiwa a ranar Alhamis a gaban Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, da Shugaban Nijar, Abdourahamane Tiani, bayan tattaunawar da suka yi a matakin shugabanni da kuma tsakanin tawagogin ƙasashen biyu a Ankara.
Daga cikin yarjejeniyoyin da aka sanya wa hannu akwai ƙa'idar aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna ta haɗin gwiwa a fannin ilimi mai zurfi tsakanin 2026 zuwa 2030.
Shugaban Majalisar Ilimi Mai Zurfi ta Turkiyya, Erol Özvar, da Ministan Harkokin Wajen Nijar, Haɗin Kai da ’Yan Nijar Mazauna Ƙasashen Waje, Bakary Yaou Sangare ne suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya.
Haka kuma, Ministan Kasuwancin Turkiyya, Ömer Bolat, da Ministan Kasuwanci da Masana’antu na Nijar, Abdoulaye Seydou, sun sanya hannu kan wata sanarwar haɗin gwiwa ta kafa Kwamitin Tattalin Arziki da Kasuwanci na Haɗin Gwiwa (JETCO).
A fannin lafiya kuwa, Ministan Lafiya na Turkiyya, Kemal Memişoğlu, da Ministan Lafiyar Jama'a da Tsaftar Muhalli na Nijar, Colonel Dr. Garba Hakimi, sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta shafi gudanarwa tare da mika ragamar Asibitin Abota na Nijar da Turkiyya.
An kuma sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Cibiyar Horar da Jami’an Diflomasiyya ta Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya da Cibiyar Nazarin Diflomasiyya da Dabarun Ƙasa ta Nijar.
Wannan yarjejeniya ta samu sa hannun Ministan Tsaron Ƙasa na Turkiyya, Yaşar Güler, da Ministan Harkokin Wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare.








![Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon](https://d2udx5iz3h7s4h.cloudfront.net/2026/4/25/67480fcc1bc16e3971fbb70d/image/35fa6aac64e41c9240c09651b2ba0fb1be4eb5b1e1ca009d1c3d191c8f65622b.webp?width=512&format=webp&quality=80)





