Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) tana ci gaba da fatan buga wasanta na shirin tunkarar Gasar Cin Kofin Duniya da ƙasar Chile, bayan da magajin garin La Linea de la Concepcion na ƙasar Sifaniya ya hana izinin gudanar da wasan saboda fargabar kiwon lafiya da ta shafi cutar Ebola.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta DR Congo ta bayyana cewa tana tattaunawa da hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya da kuma sauran hukumomin ƙasa da ƙasa da suka dace domin lalubo mafita.
Hukumomi a birnin La Linea de la Concepcion da ke kudancin Sifaniya sun sanar da matakin ƙin amincewa da wasan sada zumuntar na ranar Talata mai zuwa, inda suka kafa hujja da barazanar kiwon lafiya da za a iya fuskanta sakamakon cutar Ebola.
A ranar Laraba ne DRC ta buga wasan shirin tunkarar gasar da ƙasar Denmark a birnin Liege na ƙasar Belgium.
FIFA tana sanya ido kan cutar Ebola
Ɓullar wani nau’in cutar Ebola da ba a cika samun irinsa ba ya addabi ƙasashen DR Congo da Uganda. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana lamarin a matsayin abin damuwa na kiwon lafiyar jama’a da ya kamata duniya ta mayar da hankali akai.
Tuni dai DRC ta soke sansanin horar da ’yanwasa na kwanaki uku na shirin Gasar Cin Kofin Duniya, da kuma shirin yin ban kwana da masoya a babban birnin ƙasar, Kinshasa, saboda ɓallewar cutar a gabashin ƙasar.
Ɗaukacin ’yanwasan DRC da kocin ƙungiyar ɗan ƙasar Faransa, Sebastien Desabre, ba a ƙasar da ke tsakiyar Afirka suke zaune ba; yawancinsu suna buga wasa ne a ƙasar Faransa.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta taɓa fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa tana da masaniya kuma tana sanya ido kan lamarin da ya shafi ɓullar cutar Ebola, kuma tana tuntuɓar jami’an ƙwallon ƙafa na DRC akai-akai domin tabbatar da cewa ƙungiyar ta sami dukkan shawarwari na tsaro da na lafiya.
Cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta farko tun bayan shekarar 1974
DRC za ta buga wasa ne a Rukunin K a Gasar Cin Kofin Duniya. Za ta fafata da Portugal a wasanta na farko a Houston a ranar 17 ga watan Yuni.
Bayan haka, ƙungiyar da ake kira ‘Leopards’ za ta fuskanci Colombia a Guadalajara a ƙasar Mexico a ranar 23 ga watan Yuni, kafin ta buga wasanta na ƙarshe na rukuni da Uzbekistan a Atlanta a ranar 27 ga watan Yuni.
Cancantar shiga gasar Cin Kofin Duniya ta DR Congo ta farko tun bayan shekarar 1974, lokacin da ake kiran ƙasar da Zaire, ta haifar da gagarumin shagali na murna a faɗin ƙasar.
AFIRKA
3 minti karatu
Tawagar kwallon DRC na neman abokiyar karawa bayan Sifaniya ta fasa buga wasa da su saboda Ebola
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta ci gaba da fatan buga wasanta na shirin tunkarar Gasar Cin Kofin Duniya da ƙasar Chile, bayan da magajin garin La Linea de la Concepcion na ƙasar Sifaniya ya hana izinin gudanar da wasan saboda fargabar Ebola
Rumbun Labarai









![Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon](https://d2udx5iz3h7s4h.cloudfront.net/2026/4/25/67480fcc1bc16e3971fbb70d/image/35fa6aac64e41c9240c09651b2ba0fb1be4eb5b1e1ca009d1c3d191c8f65622b.webp?width=512&format=webp&quality=80)





