An ji ƙarar fashewar abubuwa a tsibirin Qeshm na Iran , in ji rahotannin kafafan watsa labaran ƙasar.
Rundunar Kare Juyin Juya-Halin Iran IRGC ta ce hare-haren sun mayar dahankali ne kan sansanonin sojin Amurka a Kuwait, bayan abin da ta bayyana a matsayin wani harin Amurka a kan tsibirin Qeshm a kudancin Iran.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar IRGC ta bayyana cewa dakarunta na sama sun ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka a Kuwait a matsayin martani ga abin da ta kira ƙeta ‘yancin Iran a tsibirin Qeshm.
Ta yi gargaɗin cewa duk wani ƙarin hari a Iran zai fuskanci martani “mai ƙarfi” , yana mai cewa dakarun da ke da hannu cikin ɗaukar mataki kan Iran za su fuskanci uƙuba.
Hedikwatar tsaro ta tsakiyar Amurka (CENTCOM) ta tabbatar da hare-hare kan tsibirin Qeshm .
“Dakarun Amurka sun yi nasarar kakkaɓo makamai masu linzami da jirage mara matuƙan Iran, kuma sun gudanar da hare-hare na kare kai a kan tsibirin Qeshm a matsayin martani ga ƙoƙarin kai hari da Iran ta yi a faɗin Gabas Ta Tsakiya ranar 2 ga wana Yuni,” kamar yadda CENTCOM ta wallafa a shafinta ta X.
Dakarun Amurka sun kakkaɓo jirage mara matuƙa uku masu kai hari da Iran ta tura zuwa yankin fararen hula masu tuƙin jirgi, kamar yadda ta ƙara bayyanawa.
Babu jami’in Amurka da aka ji wa rauni.
Sai dai kuma, tsarin tsaron sararin samaniyar Kuwait ya mayar da martani ga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa cikin tsakar daren Laraba, kamar yadda rundunar ta bayyana.
Rundunar sojin Kuwait ta ce ƙararrakin fashewar abubuwan da aka ji a fadin ƙasar sun faru ne sakamakon aikin kakkaɓo makamai da tsarin tsaron sararin samaniyan ƙasar ya yi.
Ba a samu ƙarin bayani ba game da lamarin nan take.
Tashe-tashen hankulan yankin sun ƙaru tun ƙarshen watan Fabrariru bayan Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare kan Iran, inda aka kashe fiye mutum 3,000 , ciki har da tshohon jagoran addinin ƙasar marigayi Ali Khamenei da wasu manyan kwamandodin soji da jami’an gwamnatin ƙasar.
Wata yarjejeniyar tsagaita wuta da Pakistan ta jagoranta ta fara aiki ranar 8 ga watan Afrilu, amma ƙoƙarin cim ma yarjejeniya mai faɗi ya ci tura kawo yanzu.












