Matatar Mai ta Dangote a Nijeriya mai ƙarfin tace gangar mai 650,000 a kowace rana tana da isasshen man jirgin sama da za ta iya fitarwa zuwa kasuwannin duniya baki ɗaya, in ji Babban Daraktan kamfanin, David Bird, a ranar Talata.
Ya ce saboda bukatar mai a nahiyar Afirka ba ta kai ta sauran yankuna ba, kuma matatar na samun rarar da za ta iya fitarwa zuwa ƙasashen waje.
“Mun yi matuƙar godiya da yadda ake kallonmu a matsayin amintacceiyar mai samar da mai mai inganci kuma abin dogaro, wanda ke iya kai kayansa cikin farashi mai sauki zuwa ko ina a duniya,” in ji Bird yayin wani taro na S&P Global Energy Middle East Petroleum and Gas Conference a birnin London.
Ya kuma bayyana cewa man jirgin sama na daga cikin nau’o’in mai da rikicin Iran da kuma rufe Mashigar Hormuz suka fi shafa sosai a baya-bayan nan.
Shirye-shiryen faɗaɗa ƙarfin tace mai
Wannan dama ce ga matatun mai da ke wajen yankin Gulf, kamar Matatar Dangote, su shiga kasuwannin duniya wajen samar da mai.
Bird ya ce matatar tana aiki a cikakken ƙarfin da aka tsara mata a halin yanzu.
Ya kuma bayyana cewa ana shirin wani aikin faɗaɗa ƙarfin matatar da ya kira “ruthless replication” domin ninka yawan abin da take tacewa.
“Za mu ƙara ƙarfin tace gangar mai 700,000 a kowace rana nan da ƙarshen shekarar 2028,” in ji Bird, yana mai cewa an riga an sayo muhimman kayan aikin da ke ɗaukar dogon lokaci kafin su iso, kuma kamfanin na kan matakin bayar da kwangilolin gine-gine.
Ya ce kungiyar na iya kaiwa ga tace gangar mai miliyan 2.1 a kowace rana idan aka ƙara wata matatar a yankin Gabashin Afirka nan gaba, wanda zai sa ta zama babbar mai taka rawa a kasuwannin danyen mai da kuma man da aka tace.
Bird ya kuma ce Nijeriya ta sauya daga fuskantar ƙarancin mai zuwa cikakken wadatar mai tun bayan fara aiki da Matatar Dangote.











