Ƙungiyar ‘yan jaridar wasanni ta duniya ta bayyana cewa akwai ‘yan jarida da dama daga ƙasar Iran da Afirka da aka hana su bizar zuwa Amurka domin ɗaukar rahoton Gasar Kofin Duniya.
Ƙungiyar ta aika wasiƙa a ranar Jumma’a ga Bryan Swanson, daraktan hulɗa da jama’a na FIFA da kuma Jochen Steinhoff, shugaban hukumar gudanarwar sashen watsa labarai na ƙwallo.
"Mun tsinci kanmu muna fuskantar wata matsala da ta daɗe tana ci gaba kuma mu ‘yan jarida ba za mu amince da ita ba: hana takardun izinin shiga ƙasa ga abokan aikinmu da aka amince da su a hukumance," in ji shugaban ƙungiyar, Gianni Merlo, kamar yadda The Athletic ta ruwaito.
"Akwai matsaloli da dama: abokan aikinmu 'yan Iran, da kuma na Afirka. Wasu daga cikinsu an ba su bizar shiga sau ɗaya kacal. Saboda haka idan ƙasarsu ta je buga wasa a Canada ko Mexico kuma suka bi tawagar, ba za su iya komawa Amurka ba. Irin waɗannan matsaloli ba su da adadi, kuma kamar yadda na faɗa, ba za a amince da su ba.
“'Yan siyasa a koyaushe suna cewa wasanni na haɗa kan jama'a kuma suna gina gada tsakanin matasa a ƙasashen da ke cikin rikici. Amma a wannan yanayin, muna tafiya ne a akasin wannan manufa.
“Muna ganin yana da muhimmanci a bai wa abokan aikinmu damar halartar gasar da yin aikinsu, domin kasancewarsu zai kasance mai muhimmanci ga martabar wasanni da abin da suke wakilta, musamman a ƙasa kamar Amurka, inda 'yancin aikin jarida ya zama wajibi.
“Ina fatan FIFA za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da an samu biza. Tuni an bar mu baya a jadawali, kuma da yawa daga cikin abokan aikinmu sun riga sun rasa damar amfani da tikitin jirgin sama da suka yanka tun da wuri. Haka kuma za su fuskanci ƙarin kuɗaɗen da ba su shirya ba."
Gasar Kofin Duniya ta FIFA mai ƙungiyoyi 48 za ta fara ranar Alhamis kuma za ta ci gaba har zuwa 19 ga Yuli, tare da wasanni a Amurka, Mexico da Canada.
Iran na cikin gasar duk da ci gaba da rikicin tsakaninta da Amurka.
Ƙasashen Afirka da ke cikin gasar sun haɗa da Aljeriya, Cape Verde, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Masar, Ghana, Côte d'Ivoire, Morocco, Senegal, Afirka ta Kudu da Tunisia.
Wasu daga cikin ƙasashen, ciki har da Côte d'Ivoire da Tunisia, suna buƙatar bizar shiga sau da yawa (multiple-entry visa) saboda suna da wasannin da za su buga a Amurka da kuma a Kanada ko Mexico.
Zuwa safiyar Asabar, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ba ta mayar da martani ba ga buƙatar yin sharhi da The Athletic ta aika mata.











