Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta sanar da kama mutum 345 da ake zargi da hannu a ayyukan daba, safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifuka daban-daban a wani samame na musamman da ta gudanar a fadin jihar cikin kwanaki uku.
Da yake jawabi ga manema labarai a Hedikwatar ’YanSanda da ke Bompai ranar Litinin, Kwamishinan ’Yansandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce an gudanar da aikin ne daga ranar 5 zuwa 7 ga Yunin 2026 bayan samun sahihan bayanan sirri da rahotannin al’umma.
A cewarsa, samamen ya gudana ne a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar, inda jami’an tsaro suka mayar da hankali kan wuraren da ake zargin masu aikata laifuka ke taruwa da kuma wuraren da ake ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
CP Bakori ya bayyana cewa baya ga kama mutum 345, rundunar ta kuma ƙwato makamai masu hatsari guda 270, ciki har da wuƙaƙe, adduna, gatari da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen aikata laifuka da tayar da zaune tsaye.
Haka kuma, ya ce an samu tarin miyagun kwayoyi da suka haɗa da tabar wiwi, ƙwayoyin Exol, Pregabalin, da madarar sukudaye wato “Suck and Die” da Turanci, tare da wasu nau’ikan kayan maye daban-daban.
Kwamishinan ya bayyana cewa wannan nasara ta taimaka wajen daƙile ayyukan daba, rage ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da kuma hana wasu manyan laifuka kamar fashi da makami da ƙwacen waya.
Ya danganta nasarar da aka samu da aikin Operation Kukan Kura, wanda ke ƙara yawan sintiri a sassan jihar, da kuma sabon Sashen Yaki da Manyan Laifuka (VCRU), wanda ya ƙara wa rundunar ƙarfin tattara bayanan sirri da kuma saurin kai dauki lokacin gaggawa.
Kwamishina Bakori ya jaddada cewa rundunar ba za ta yi sassauci ga masu aikata laifuka ba, yana mai gargadin cewa duk wanda ya ci gaba da shiga harkokin daba ko ta’ammali da miyagun ƙwayoyi zai fuskanci hukuncin doka.
Ya kuma ce yanzu haka ana binciken mutane 345 ɗin da aka kama, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.
A karshe, shugaban ’yansandan ya yaba wa gwamnatin jihar da al’ummar Kano bisa hadin kai da bayar da bayanan sirri, yana mai kira ga jama’a da su ci gaba da sanar da jami’an tsaro duk wani motsi ko abu da suke zargi domin kara tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.


.jpeg?width=720&format=webp&quality=80)



.jpeg?width=128&format=webp&quality=80)








