| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Ɓarayin daji sun yi garkuwa da gomman mutane a Jihar Zamfara bayan sun gayyace su tattaunawar sulhu
An kama gomman mutane mafi yawancinsu dattijai a Jihar Zamfara ta arewa maso yammacin Nijeriya bayan 'yanbindiga sun gayyace su tattaunawar zaman lafiya.
Ɓarayin daji sun yi garkuwa da gomman mutane a Jihar Zamfara bayan sun gayyace su tattaunawar sulhu
TSOHON HOTO: Yayin da soji ke aikin daƙile aika-aikar 'yan bindiga wasu alummomi a ƙasar na ƙoƙarin tattaunawa da 'yan bindigar. / Reuters

‘Yanbindiga a Jihar Zamfara a arewa maso yammacin Nijeriya sun tsare gomman mutanen ƙauye waɗanda suka gayyata zuwa wani zama game da yiwuwar yarjejeniyar zaman lafiya , kamar yadda hukumomi da mazauna suka bayyana ranar Litinin, lamarin da ke bayyana taɓarɓarewar tsaro a yankin.

Rundunar ‘yansandan jihar ta ce an kama mutum 39 ranar Lahadi a lokacin da suka je wani zama a daji kusa da Magamin Diddi a ƙaramar hukumar Maradun a jihar Zamfara. Wasu mazauna wurin da jami’ai sun ce adadin mutane zai iya kaiwa 50.

Wata sanarawar da rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta fitar ta ce waɗanda lamarin ya shafa suna tattaunawa da ‘yan’uwan shugaban ‘yanbindigan ne a domin cim ma yarjejeniyar zaman lafiya da rage ƙuntatawa ta hana tafiye-tafiye kan al’ummar yankin a lokacin da lamarin ya auku.

Zamfara ɗaya ce daga cikin wuraren da matsalar tsaro ta fi ƙamari inda ƙungiyoyin ‘yanbindiga suke garkuwa da mutane da yawa da kashe-kashe da kai samame ƙauyuka . Tashin hankalin ya hana noma ya kuma raba dubban mutane da gidajensu.

Dakaraun tsaro sun tura jami’ai da kayayyakin tattara bayanai domin gano inda mutanen suke, a cewar sanawar rundunar ‘yansandan.

An ba da rahoton cewa an sako wasu mutane domin su isar da saƙon adadin kuɗin fansan da masu garkuwa da mutanen ke buƙata daga ƙauyen.

Wani mazaunin ƙauyen na Magamin Diddi, ya ce ‘yanbindigar suna buƙatar naira miliyan 125 ($91,880) domin sakin waɗanda aka yi garkuwar da su.

Al’ummomin yankin da dama sun koma tattaunawa kai-tsaye da ‘yanbindiga domin samun damar zuwa gonankinsu ko kuma sako waɗanda aka kama, wani matakin da hukumomi ke ƙoƙarin hanawa, amma aka gaza hanawa gabaɗaya.