Yayin da za a fara Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 ranar 11 ga Yunin 2026 a ƙasashen Amurka, Canada, da Mexico, FIFA ta fito da sabbin dokokin ƙwallo da dama za su fara aiki a gasar.
Ga biyar daga cikin manyan sauye-sauyen doka da a za a gani a ƙwallon ƙafa a gasar da kuma a sauran gasannin ƙwallo na duniya, daga 1 ga Yulin 2026.
Dokar barin filin wasa
Daga yanzu FIFA ta yanke cewa duk ‘yanwasan da suka fice daga filin wasa saboda nuna ƙorafi kan hukuncin alƙalin wasa, to sun sallama wasan kenan, sun yi rashin nasara.
Wannan zai magance irin taƙaddamar da aka gani a wasan ƙarshe na AFCON 2025, inda ‘yanwasan Senegal suka fice daga fili saboda adawa da bugun fanareti da aka bai wa Maroko.
Dokar rufe baki yayin ce-ce-ku-ce
Duk ɗanwasan da ya rufe bakinsa da hannu, ko damtse, ko da rigarsa yayin da suke cacar-baki da wani a fili, to za a ba shi jan kati.
Kai-tsaye dokar za ta magance irin tankiyar da aka yi lokacin da ɗanwasan Benfica, Gianluca Prestianni ya yi ce-ce-ku-ce da Vinicius Jr na Real Madrid, har ya zagi Vini bayan ya ja kwalar rigarsa don rufe bakinsa.
Amma dokar ba za ta yi aiki kan ‘yanwasan da suke rufe bakinsu yayin tattaunawar da ba ta faɗa ba.
Dabarar cunkushewa (“set piece”)
Sanya ido kan salon tsayar da wasa don saita ‘yanwasa su cunkushe ragar abokan karawa don hilatar su, yadda za su ciyo ƙwallo da zarar an buga ta.
Wannan wata dabarar cin ƙwallo ce da ta yi suna a gasar Firimiya ta Ingila, kuma ana kiranta da “set piece” a Ingilishi. Irin wannan dabara ce Arsenal ta yi amfani da ita har ta ci ƙwallaye 25 a gasar Firimiyar bana kuma ya kai ta ga lashe kofin.
Hakanan, hukumomin FIFA da na IFAB, mai kula da dokokin buga ƙwallo, sun fito da dokar hana ture da tunkuɗe yayin amfani da wannan dabarar.
Dokar hana tare gaban masu tsaron raga
Za a fara aiki da sabuwar dokar da za ta hukunta ‘yanwasan da suka tare abokan karawa daga buga ƙwallo yayin bugun firikik da kwana.
An kwafo wannan dokar ne daga wasan ƙwallon kwando, wadda ta hana ‘yanwasa su zama katangar hana taɓa ƙwallo. A yanzu za a hukunta ɗanwasan da ya aikata wannan tun gabanin a buga kwanar ko firikik ɗin.
Dokokin rage ɓata lokaci
Daga yanzu za a bai wa ‘yanwasa sakanni 10 su fita daga filin wasa idan an yi canji. Idan ya haura sakan 10, to ba za a bari sabon ɗanwasan ya shiga fili ba har sai bayan minti ɗaya kuma sai idan an tsayar da ƙwallo.
Haka nan, alƙalan wasa za su bai wa ɗanwasa sakan 5 ne kacal ya buga ƙwallo bayan ta tsaya a fili, ko lokacin turoyin ko kwana. Idan ba haka ba, to za a bai wa ɗayar ƙungiyar bugun.
Sannan an haramta wa koci ya yi ta zantawa da ‘yanwasansa yayin da gola ke samun kulawar jami’an lafiya yayin wasa.










