Uganda ta yi suka ga takunkumin zirga-zirgar jiragen sama da wasu ƙasashe, ciki har da Amurka, suka ƙaƙaba mata saboda ɓarkewar cutar Ebola wadda ta bazu daga ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da ke maƙwabtaka, tana cewa wannan takunkumi bai dace ba.
An yaba da yadda ƙasar ta gabashin Afirka ta mayar da martani ga sabuwar ɓarkewar wannan mummunar cutar inda mutane biyu suka mutu daga cikin mutum 19 waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar a ƙasar, tun lokacin da aka yi gargaɗi a DRC a tsakiyar watan Mayu.
Kusan dukkan su 'yan ƙasar Kongo ne da suka ketare iyaka daga ƙasar su, inda aka tabbatar da fiye da mutum 676 sun kamu da cutar sannan kuma aka tabbatar da mutuwar 136 tun daga 15 ga Mayu.
“A yau, Ma'aikatar Lafiya ta Uganda tare da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta ƙasa, Jakadu, da masu aikin kamfanonin jiragen sama da ke aiki a Uganda, sun tattauna game da takunkumin tafiya na rashin adalci da aka saka kan Uganda saboda halin da ake ciki na Ebola,” in ji Diana Atwine, sakatariyar dindindin ta ma'aikatar lafiya, a saƙon da ta wallafa a shafinta na X a ranar Jumma'a.
Babu allurar rigakafi ko magani
“Duk da mun fahimci buƙatar a kasance masu taka tsantsan, saka takunkumi ido rufe yana rage ƙwarin gwiwar da ƙasashen ke da shi na bayar da rahoto a fili na ɓarkewar cutar , ba tare da la’akari da ainahin barazanar haka ba.”
Baya ga Amurka, Canada da Hadaddiyar Daular Larabawa suna daga cikin ƙasashen da suka saka haramcin shiga ga matafiya daga Uganda, DRC da makwabtan Sudan ta Kudu sakamakon ɓarkewar.
Yayin da shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yaba da dabarun Kampala a ziyarsa ta Uganda ranar Litinin, hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗi a ranar Jumma'a cewa ɓarkewar na yaduwa zuwa sabbin yankuna a maƙwabtan DRC.
Babu allurar rigakafi ko magani na musamman ga nau'in Ebola na Bundibugyo da ke haddasa wannan sabuwar ɓarkewar, wadda ita ce ta 17 da ta afku a wannan babbar ƙasar tsakiyar Afirka.
Ana yada cutar ta hanyar kusantar jiki da ruwan jiki mai ɗauke da ƙwayoyin cuta; a cikin shekaru 50 da suka gabata cutar ta kashe mutane fiye da 15,000 a Afirka.









