Manoma da makiyaya daga al’ummomi da dama a yakin Maradi na Jamhuriyyar Nijar sun sanya hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya bayan shafe watannni ana takaddama da kokarin sulhu da nufin kawo karshen rikice-rikicen da ke ci gaba da faruwa tare da lalubo mafitar tabbatar da amfani da kwarin Goulbi Maradi mai albarka cikin lumana.
An cim ma yarjejeniyar ne a ranar 9 ga Yunin 2026 a yankin Sarkin Yamma inda wakilan manoma da makiyaya daga gundumomin Safo da Sarkin Yamma da kuma Tibiri da birnin Maradi suka sanya hannun kan yarjejeniyar.
Gwamnan Yankin Maradi, da Kontrolan 'Yansanda Issoufou Mamane ne suka jagoranci taron yarjejeniya, kazalika Sarkin Katsina-Maradi, Ahmed Ali Zaki, tare da sarakunan gargajiya, da jami'an yankin, da shugabannin al'umma da kuma hukumomin tsaro duk sun samu halarta.
Yarjejeniyar zaman lafiyar ta samo asali ne daga zaman sulhu na tsawon watanni takwas wanda Cibiyar Jinƙai ta Shiga Tsakani (HD) ta shirya bisa bukatar hukumomin yankin da shugabannin gargajiya.
A tsawon lokacin, an ƙarfafa wa manoma da makiyaya gwiwa don su iya gane hanyoyin magance takaddamar da ta daɗe tana tasowa a tsakani kan filaye, ruwa da albarkatun kiwo a kwarin.
An shafe shekaru da dama, ana takaddama kan albarkatun ƙasa wanda ke janyo tashe-tashen hankula tsakanin manoma da al'ummomin makiyaya a Maradi.
Kazalika yawan ƙaruwar jama'a, da kwararowar hamada, da sauyin yanayi, da ruwan sama da fari da kuma ambaliyar ruwa duk sun taimaka wajen ƙara matsi ga raguwar albarkatun yankin, yanayin da ya zama tushen rikici
Haka kuma Gwamna Issoufou Mamane ya bayyyana cewa rikice-rikicen a wasu lokutan sukan haifar da tashin hankali da asarar rayuka, tare da janyo rashin tsaro a tsakanin al'ummomin karkara.
Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani shiri da ya zo a kan lokaci, kuma wanda ya dace da ƙoƙarin da Nijar ke yi na haɓaka hanyoyin samun daidaito da dawo da zaman lafiya a tsakanin al'ummomi.






