An fara Gasar Cin Kofin Duniya inda ƙasar Mexico ɗaya daga masu masaukin baƙi ta fara wasan da ƙafar dama, ta doke Afirka ta Kudu 2-0 a gaban magoya baya 80,000 a filin wasa na Estadio Azteca a birnin Mexico City.
Julian Quinones ne ya fara zura ƙwallo a minti na tara da take leda a wasan buɗe gasar a ranar Alhamis, abin da ya tabbatar da yadda Mexico ta riƙe wasa tun farko a cikin filin da aka buga wasannin ƙarshe na 1970 da 1986.
Raul Jimenez ya zura ƙwallo ta biyu ga Mexico. Bayan wakiltar tawagar Mexico a Gasar Kofin Duniya sau huɗu, a ƙarshe ya samu wannan ƙwallo ta farko da ya daɗe yana nema.
Fara wasan ya ƙaddamar da wata gagarumar gasar da ke da ƙasashe 48 wacce za ta ɗauki kusan makonni shida.
Manyan nune-nunen bikin buɗe gasar da Amurka, Mexico da Kanada masu masaukin baƙi suka gudanar shi ne mafi girma a tarihin Gasar Kofin Duniya. Za ta ci gaba har zuwa wasan ƙarshe a New Jersey a ranar 19 ga Yuli, kuma ana hasashen za ta samar da kuɗaɗen shiga da ya kai dala biliyan 13 gaba ɗaya.
Bikin buɗe gasar ya haska filin wasa na Estadio Azteca kafin fara wasan, inda tauraruwar Colombia Shakira da mawakin Nijeriya Burna Boy suka nishaɗantar da ‘yan kallo da rera "Dai Dai", waƙar gasar a hukumance.
Amma an samu turereniya a wajen filin, yayin da magoya baya ke dannawa da tura juna suna ƙoƙarin shiga yankin da aka ware wa magoya baya a tsakiyar birnin Mexico.
Tururuwar da aka yi wajen shiga filin wasan zai kasance abin da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya FIFA za ta yi farin ciki da shi, wadda ta fuskanci suka mai tsanani kan tsadar tikiti.




.jpeg?width=512&format=webp&quality=80)






