| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya ta yi tur da zargi marar tushe da mai kisan ƙare-dangi Netanyahu ya yi wa Shugaba Erdogan
Turkiya ta ce za ta ci gaba da magana a kan Netanyahu da abokansa kuma za ta bi hanyoyin shari'a na duniya don samun amincewa.
Turkiyya ta yi tur da zargi marar tushe da mai kisan ƙare-dangi Netanyahu ya yi wa Shugaba Erdogan
Turkiyya ta yi tur da zargi marar tushe da mai kisan ƙare-dangi Netanyahu ya yi wa Shugaba Erdogan

Turkiyya Ta Yi Watsi Da Zarge-Zargen Netanyahu Kan Shugaba Erdogan

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi kakkausar suka kan abin da ta bayyana a matsayin “zarge-zarge marasa tushe, na tsokana kuma marasa gaskiya” da aka yi wa Shugaba Recep Tayyip Erdogan, tana mai cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, na ƙoƙarin yaudarar ra’ayin jama’ar duniya.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ranar Laraba, ta ce zarge-zargen da aka yi wa Erdogan wani yunƙuri ne daga Netanyahu da na kusa da shi na karkatar da hankalin duniya daga ayyukansu.

“Waɗannan zarge-zarge marasa tushe, na tsokana kuma na ƙarya da aka yi wa Shugabanmu mai girma ba komai ba ne illa wani yunƙuri na Netanyahu da abokan tafiyarsa na yaudarar ra’ayin jama’ar duniya,” in ji sanarwar.

Ma’aikatar ta kuma ce “ƙaryar da Netanyahu, wanda ta kira ƙwararren mai aikata kisan kiyashi, ke amfani da ita domin ɓoye gaskiya ba za ta iya kawar da alhakinsa kan manyan laifukan da ake zarginsa da aikatawa ba.”

Ta jaddada cewa Turkiyya za ta ci gaba da bayyana abin da take kira gaskiya game da Netanyahu da waɗanda ke tare da shi, tare da neman a hukunta su ta hanyoyin shari’a na ƙasa da ƙasa.

“A matsayinmu na Turkiyya, za mu ci gaba da bayyana gaskiyar da ta shafi Netanyahu da abokan aikinsa ba tare da wata-wata ba. Haka kuma za mu ci gaba da ƙoƙarin ganin an gurfanar da su a gaban kotunan ƙasa da ƙasa saboda ayyukan da suka saɓa wa doka da ƙa’idodin ɗan Adam,” in ji sanarwar.

A wani bangare kuma, Shugaba Erdogan ya bayyana cewa hare-haren da Isra’ila ke kai wa a ƙasashen Syria da Lebanon sun kai wani mataki da suke barazana ga Turkiyya ma.

Ya ce abin da ya kira “ta’addancin” Isra’ila na zama barazana ga duniya baki ɗaya, kuma wajibi ne a dakatar da shi.

Shugaban ya kuma yi magana kan abin da ya kira ruɗin samar da “Ƙasar Alkawari”na Isra’ila, yana mai cewa Turkiyya na sane da manufar da ke bayan hakan.

“Da yardar Allah, ba za mu taɓa bari hakan ya faru ba,” in ji Erdogan.