Wata kotun Amurka ta yi wa wani tsohon kwamandan Taliban ɗaurin shekaru 42 ranar Talata da kuma shekara biyar na saki da sa ido domin rawar da ya taka wajen garkuwa da mutane, ciki har da wani ɗanjaridar Amurka, wanda aka bayyana sunansa a matsayin ɗanjarida David Rohde na Jaridar New York Times .
Wata kotun New York ce ta yi wa Haji Najibullah mai shekara 50 din ɗaurin domin “rawar da ya taka wajen kama wani ɗanjaridar Amurka da ‘yan Afghanistan biyu a Afghanistan da Pakistan a shekarar 2008 da 2009,” kamar yadda wata takardar koru ta bayyana.
An kuma ɗaure shi sakamakon rawar da ya taka wajen jagorantar mayaƙan Taliban da suka ƙaddamar da hare-hare kan jami’an sojin Amurka a Afghanistan tsakanin shekarar 2007 da shekarar 2009, lamarin da ya haddasa mace-macen sojojin Amurka.
Bayan an kama shi a ƙasar Yukraine, an mayar da shi zuwa Amurka a shekarar 2020.
An kama shi ne ranar 25 ga watan Afrilun shekarar 2025, sannan Najibullah ya amsa laifin garkuwa da mutane da kuma ba da taimako na kaya ga ayyukan ta’addanci da suka haddasa mutuwa, in ji takardar.
“Waɗanda suka ji wa Amurkawa ciwo kuma suka taka rawa a ta’addanci za mu yi farautarsu da kuma gurfanar da su a gaban kotu, komin daɗewa,” in ji muƙaddashin Antoni Janar Todd Blanche, kamar yadda takardar ta ambato.
“A matsayinsa na kwamandan Taliban, Najibullah ya taimaka wa hare-haren ta’addanci mara tausayi da suka kashe jami’an sojin Amurka da kuma kitsa garkuwa da mutane mara tausayi kan wani ɗanjarida Ba’amurke da fararen hula ‘yan Afghanistan biyu.
Ɗaurin yau ya ba da hukuncin gaskiya ga waɗanda lamarin ya rutsa da su da iyalansu.”
An yi garkuwa da Rohde ne a ƙasar Afghanistan cikin watan Nuwamban shekarar 2008, tare da wani tafinta da wani direba.
Jaridar Times, ta samu ta ɓoye labarin garkuwa da shi domin kada ta yi barazana ga rayuwarsa, inda Rohde ya samu ya tsere daga wadanda suka yi garkuwa da shi a watan Yunin shekarar 2009.












