Mutum 49 sun rasu a cikin hamadar Sahara a wani wuri a ƙasar Nijar bayan motar da ke ɗauke da su ta lalace, kamar yadda hukumomi suka bayyana ranar Alhamis.
Mamatan na cikin waɗanda ke dawowa daga ƙasar Mali domin bukukuwan Babbar Sallah a lokacin da motarsu ta lalace, sannan ruwansu ya ƙare, kamar yadda ofishin gwamnan Jihar Agadez ya bayyana a wani saƙon da ya wallafa a shafin Facebook.
Mutanen 49 “sun mutu ne sakamakon ƙishirwa a wani wuri mai nisan fiye da kilomita 80 yamma da garin Assamaka”, in ji saƙon. Assamaka wani muhimmin wurin ƙetarewa ne tsakanin Nijar da Aljeriya da Mali, ko da yakeya fi kusa da iyakar Mali.
“Bayan sun rasa ruwa kuma suka kasa gyara motarsu duk da ƙoƙarin direban da yaransa da fasinjojin, matafiyan sun sami kansu a maƙale a tsakiyar wani wuri mai wuyar sha’ani, inda yanayi mai tsanani da kuma rashin wurin samun guzuri ya sa rayuwa ta yi wahala matuƙa,” kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.
Tuni dai aka binne mutanen a ƙabarin bai-ɗaya a cewar sanarwar.
Sai dai kuma mutum biyu daga cikin waɗanda suke cikin jama’ar sun tsira, bayan sun yi tafiyar fiye da kilomita 50 da ƙafa zuwa wani wuri, inda suka samu ruwa sannan kuma suka nufi Assamaka, inda mutanen biyu suka sanar da hukumomi, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.









![Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon](https://d2udx5iz3h7s4h.cloudfront.net/2026/4/25/67480fcc1bc16e3971fbb70d/image/35fa6aac64e41c9240c09651b2ba0fb1be4eb5b1e1ca009d1c3d191c8f65622b.webp?width=512&format=webp&quality=80)



