Batutuwa biyar da Shugaba Tinubu ya taɓo a Ranar Dimokuradiyya ta Nijeriya ta 2026
NIJERIYA
3 minti karatu
Batutuwa biyar da Shugaba Tinubu ya taɓo a Ranar Dimokuradiyya ta Nijeriya ta 2026Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa tana samar da ababen more rayuwa kamar hanyoyi da za su haɗa cibiyoyin da ake samar da abubuwa da kuma kasuwanni.
Tinubu ya faɗi wannan ne a jawabin bikin ranar Dimokraɗiyya da ya yi wa 'yan ƙasar / AP

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi jawabi ga 'yan ƙasar, don murnar ranar Dimokuraɗiyya ta ƙasar ta 2026, wanda daga bisani mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X.

Ga muhimman batutuwa da Shugaban y ambata a jawabin nasa:

Miƙa-wuyan ‘yanta’adda

Shugaba Tinubu ya yi kashedi da ‘yanbindiga da masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyin ta’addanci, yana cewa, “Ku miƙa wuya ko kuma ku fuskanci cikakken ƙarfin gwamnatin Nijeriya. Wannan damar miƙa wuyan ba za ta kasance a buɗe har abada ba”.

“Babu tausayi da za a nuna wa waɗanda suke ciniki da jinin ‘yan Nijeriya,” in ji shi.

Shugaban ya ce ƙasar ta bar matakin neman horarwa daga ƙasashen Amurka da Faransa da sauran ƙasashen Turai, zuwa matakin kai harin mara kuskure kan ‘yanta’adda.

“A Arege, jihar Borno, mun kassara cibiyar ba-da umarni ta ISWAP. Mace-mace masu alaƙa sun ragu da kashi 81 cikin 100 tun shekarar 2015. An kassara fiye da ‘yanta’adda 13,000 a cikin shekarar da ta gabata,” a cewar shugaban.

“Amma ƙofar miƙa-wuya a buɗe take. Fiye da mayaƙa 124,000 da iyalansu ne suka ajiye makamansu tun shekarar 2023, ƙarƙashin shirin Operation Safe Corridor,” in ji Tinubu.

Laifi ba shi da ƙabila

Sai dai kuma, shugaban ya ja hankalin ‘yanƙasar a kan hatsarin da ke cikin alaƙanta laifi da wata ƙabila

“A lokaci irin wannan, ka da mu ringa ɗora wa wasu laifi. Laifi ba shi da ƙabila. Dole mu haɗa-kai kuma mu kasance da tabbacin cewa maƙiyan ƙasarmu za su zama tarihi nan ba da jimawa ba,” in ji shi.

“Za mu yi nasara kan ta’addanci kuma za mu ci gaba da gina ƙasa mai wadata,” in ji shi.

Shawara ga matasa

Shugaba Tinubu ya yi kira ga matasa, yana cewa, “Ga matasanmu, Nijeriya ƙasarku ce kuma makomarku ce. Ku yi gini a nan, ku haɗa manhajoji a nan, ku yi aiki a nan, kuma ku yi zaɓe a nan.”

“A ko wace babbar ƙasa, waɗanda suka tsaya a gida, suka tsaya domin warware matsalolinta su ne suke gina ta, ba waɗanda suka yi watsi da ita ba,” in ji shugaban.

Gyaran tattalin arziƙi

Shugaba Tinubu ya ce gyaran da gwamnatinsa take yi wa tattalin arziƙin ƙasar yana samar da daidaito da ƙwarin-gwiwa na masu zuba jari a Nijeriya.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa tana samar da ababen more rayuwa kamar hanyoyi da za su haɗa wuraren da ake samar da abubuwa da kasuwanni.

Sai dai kuma, shugaban ya ce duk da ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar, ‘yan ƙasar da dama na fama da fatara.

“Duk da haka, ‘yan Nijeriya da yawa suna fama da matsin tattalin arziƙi,” in ji shi.

“Mun mayar da hankali wajen rage hauhawar farashin da faɗaɗa yawan samar da ababe da samar da ayyukanyi da inganta rayuwa da kuma ƙarfafa ƙwarin gwiwa kan tattalin arziƙinmu da samar da yanayi na wadata mai ɗorewa,” a cewar Tinubu.

‘Yancin ƙananan hukumomi

Shugaban ya ce saboda dimokuraɗiyya na fama da zagon-ƙasa idan mutane ba su ji ta a aljihunsu ba, shi ya sa gwamnatinsa ta nemi cin gashin-kai na kuɗi ga ƙananan hukumomi 774 na ƙasar.

“Wani muhimmin ƙalubale ga cigaban ƙasarmu shi ne aikin ƙananan hukumomi mara tasiri. Rashin tsaron da muke yaƙa yanzu, raunin gwamnati a matakin karkara na cikin ababen da suka janyo shi,” in ji shi.

Shugaban ya ce kowane ƙarni na mutanen kuma kowane zamani na tare da ƙalubalensu, inda ya ce ƙalubalen da ke gaban ‘yan Nijeriya na wannan zamanin shi ne tabbatar da wadata.