A ranar Laraba, wasu Yahudawa 'yan-kama-wuri-zauna sun banka wa wasu sassa na masallatai biyu wuta a ƙauyukan Jiljilya da Mazra’a al-Nubani, da ke arewacin birnin Ramallah a yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila aka mamaye. Haka kuma sun rubuta wasu kalmomi da harshen Ibrananci a jikin bangon masallatan.
Majiyoyin yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa wasu daga cikin mazaunan matsugunan sun kutsa cikin ƙauyen Jiljilya da asubahin ranar, inda suka banka wa masallacin ƙauyen wuta.
Wutar ta ƙone sashen da mata ke gudanar da sallah tare da jawo lalacewa a bangon wajen masallacin.
Majiyoyin sun ce a baya-bayan nan ƙauyen Jiljilya na fuskantar ƙarin hare-hare daga mazaunan matsugunan Yahudawa.
A watan da ya gabata ma, sun kai hari ƙauyen tare da sace garken tumaki mallakin wasu Falasɗinawa mazauna yankin.
A wani hari daban, 'yan-kama-wuri-zaunan sun kutsa cikin ƙauyen Mazra’a al-Nubani inda suka banka wa wani masallaci wuta, lamarin da ya haddasa asarar dukiya.
A dukkan ƙauyukan Jiljilya da Mazra’a al-Nubani, maharan sun kuma rubuta wasu kalmomi da harshen Ibrananci a jikin bangon masallatan.
Tun bayan fara yaƙin Isra’ila a Gaza a watan Oktoban 2023, yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye ya shaida karuwar hare-haren da sojojin Isra’ila da kuma mazaunan matsugunan Yahudawa ke kai wa Falasɗinawa da dukiyoyinsu.
Hare-haren sun haɗa da ƙone-ƙone, ƙwace filaye, da hana manoma shiga gonakinsu, musamman a yankunan da ke kusa da matsugunan Yahudawa.
A cewar alkaluman hukumomin Falasɗinu, rikicin da ake fama da shi a Yammacin Kogin Jordan ya yi sanadin kashe Falasɗinawa 1,169, ya jikkata 12,666, yayin da aka kama kusan 23,000 tare da raba kusan 33,000 da muhallansu.













.jpeg?width=512&format=webp&quality=80)
