Magajin garin babban birnin Rasha ya ce wasu jirage marasa matuƙa sun samu sun kai ga wata babbar matatar mai kuma "ana ɗaukar matakai na magance tasirin" harin, ba tare da bayyana ko an lalata matatar ba.
Moscow ta kasance tana daƙile wani "babban hari" na jirage mara matuƙa daga Yukren, inda wasu jirage mara matuƙa suka kai ga wata matatar mai , kamar yadda magajin garin birnin Sergey Sobyanin ya bayyana ranar Alhamis.
Kiev ta zafafa hare-hare kan Rasha cikin ‘yan watannin da suka gabata, inda take yawan afka wa kayayyakin mai da kuma cibiyoyin fitar da ababe ƙetare na ƙasar a wani yunƙuri na tsotse muhimmin kuɗaɗen shiga na mai da ke ɗaukar nauyin ƙoƙarin yaƙin Moscow wanda a halin yanzu yana shekararsa ta biyar.
"Dakarun tsaron sama suna ci gaba da tunkuɗe wani hari mai yawa. Wasu jirage mara matuƙa sun samu sun kai ga MNPZ," wata muhimmiyar matata a babban birnin Rasha, kamar yadda Sobyanin ya rubuta a manhajar Telegram.
Magajin garin ya ce "ana ɗaukar matakai domin magance tasirinsu", ba tare da bayyana ko matatar da lalace ba.
Sobyanin ya ce kafin ƙarfe na safiya 7:00 na birnin (ƙarfe 0400 agogon GMT) tsarin tsaron sararin samaniyar Rasha ya lalata jirage mara matuƙa 43 a cikin dare.
Wani harin jirgi mara matuƙa na Ukraine a ranar Talata ya haddasa gobara a wata muhimmiyar matatar mai a wajen Moscow kuma ya haddasa lalata abubuwa.
Amma bai bayyana ba ko matatar ce aka sake kai wa hari ranar Alhamis.
Tun da yaƙin ya ɓarke a shekarar 2022, Rasha ta yi ta kai hari kan Ukraine inda take kai samame ta sama da jirage mara matuƙa da makamai masu linzami, yayin da ƙoƙarin diflomasiyya da Washington ke jagoranta na kawo ƙarshen rikicin ya ci tura domin yaƙin da ake a Gabas Ta Tsakiya.













