| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
Mutane uku sun mutu bayan motar fasinja ta yi karo da giwa a gandun dajin Uganda
Motar tana ɗauke da ma'aikatan Hukumar Haraji ta Uganda.
Mutane uku sun mutu bayan motar fasinja ta yi karo da giwa a gandun dajin Uganda
Ana samun rahotannin haduwa tsakanin mutane da namun daji a fadin al'ummomin karkara na Gabashin Afirka. / Getty Images

Wata motar fasinja ta kaɗe giwa a gandun dajin Uganda, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane uku sannan wasu huɗu suka jikkata, in ji 'yan sanda.

Wata sanarwa da 'yansanda suka fitar a ranar Litinin tace, hatsari ya auku a ranar Lahadi a kan titin da aka shimfida a cikin Gandun Daji Murchison Falls na Ƙasa.

Motar na ɗauke da ma'aikatan Hukumar Haraji ta Uganda waɗanda suke tafiya daga wani birni a arewacin Uganda zuwa Kampala, babban birnin ƙasar.

Sanarwar 'yan sandan ta ce, bayan kaɗe dabbar, direban “ya kasa sarrafa motar". "Ana kira ga direbobi su yi taka-tsantsan matuƙa yayin tuki a cikin gandunan daji na ƙasa da yankunan da ake killace namun daji."

Bidiyon da aka ɗauka a wurin ya nuna mutanen da ke cikin motar da ta lalace suna kukan neman agaji, yayin da giwar da ta ji rauni ke ƙoƙarin tashi daga cikin ciyayi da ke kusa. Ba a tabbatar ko giwar ta rayu ba.