| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Jami'an leƙen asirin Turkiyya sun kama mutum 10 da ake zargin 'yanta'addan Daesh ne a Syria
Aikin wanda aka yi shi tare da haɗin gwiwar Hukumar Leken Asiri ta Syria, ya kai ga kamo waɗanda ake zargin ‘yan ta’addan Daesh ne har mutum goma, waɗanda daga bisani aka miƙa wa hukumomin Turkiyya.
Jami'an leƙen asirin Turkiyya sun kama mutum 10 da ake zargin 'yanta'addan Daesh ne a Syria
MIT ta gudanar da samame na hadin gwiwa da hukumar leken asiri ta Syria / AA

Hukumar Leƙen Asiri ta Turkiyya (MIT) ta kai samame a ƙasar Syria inda ta kama waɗanda ake zargin ’yan ta’addar Daesh ne da ke cikin jerin waɗanda ake nema ruwa-a-jallo a matakin kasa da kasa, in ji majiyoyin tsaro a ranar Asabar.

Aikin wanda aka yi shi tare da haɗin gwiwar Hukumar Leken Asiri ta Syria, ya kai ga kamo waɗanda ake zargin ‘yan ta’addan Daesh ne har mutum goma, waɗanda daga bisani aka miƙa wa hukumomin Turkiyya.

Biyo bayan matakan shari'a da tambayoyi, an kama tara daga cikin waɗanda ake tuhuma a hukumance, yayin da aka tsawaita tsare ɗaya daga cikinsu har sai an sake duba batun.

Majiyoyi sun bayyana cewa MIT ta gano wadanda ake zargin asalinsu Turkawa ne waɗanda suka yi tafiya zuwa Syria a cikin 'yan shekarun baya kuma suka shiga ƙungiyar ta'addanci ta Daesh da ke aiki a yankin.

Bincike kuma ya nuna cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin yana da alaƙa da waɗanda ke da alhakin harin tashar jirgin ƙasa na Ankara a 2015, wanda ya kashe mutane 109.

Yayin tambayoyi, waɗanda ake zargin sun bayyana tsarin yadda Daesh ke ɗaukar sabbin mambobi da ba su horo, ciki har da horon makamai, shigar da aƙida, da ayyukan yaɗa labarai da aka tsara a ƙasashen waje.

A cikin waɗanda aka kama akwai manyan jami'ai na ƙungiyar, waɗanda aka gano a matsayin Ali Bora, Omer Deniz Dundar, Huseyin Peri, Kadir Gozukara, Abdullah Cobanoglu, Hakki Yuksek, Kadir Demir, Cekdar Yilmaz, Murat Ozdemir da Ishak Gunci, waɗanda suka riƙe muƙamai a tsarin umarni na Daesh a ƙasashen waje.

Majiyoyin tsaro sun ruwaito cewa waɗanda ake zargin sun yi aiki a fannoni daban-daban na Daesh a Syria, ciki har da sassan dabaru (logistics), kafofin watsa labarai, lafiya da sassan gudanarwa.

Ana ci gaba da matakan shari'a, yayin da bincike ke kara fadada zuwa wasu ƙananan ƙungiyoyi masu alaƙa da Daesh waɗanda ake danganta su da hare-hare na baya a cikin jihohi da dama.