Dubban ɗaruruwan Musulmai daga fadin duniya sun fara gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 1447/2026 a ranar Litinin 8 ga watan Zul-Hijjah, inda suka fara kwarara zuwa Mina, birnin tantuna. Wannan rana ita ce rana ta farko ta gudanar da ayyukan Hajji, wacce ake kiranta da Ranar Tarwiyah.
Fuskokin mahajjata cike suke da farin ciki da ƙanƙan da kai yayin da suke barin masaukansu na birnin Makka, maza suna sanye da fararen tufafin harami, mata kuma sunye da tufafin da ke rufe musu jikinsu, suna masu rera kalmar "Labbaikallahumma Labbaik".
Sai dai alhazan ƙasashe da dama sukan fara tafiya zuwa Mina tun cikin dare, inda suke wayar garin ranar takwas ga wata a can.
Kimanin mahajjata miliyan biyu ne ake sa ran za su yi aikin hajjin na bana, kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Kasar Saudiyya ta yi hasashe.
Muhimmancin Ranar Takwas ga Wata
Aikin Hajji na ɗaya daga shikashikan Musuluci guda biyar.
Ranar Tarwiyah ita ce ranar da ake fara aikin Hajji. A wannan rana, mahajjata suna gudanar da waɗannan abubuwan:
Sanya harami da ƙulla niyya, musamman ga masu aikin Hajji nau’in tamattu’i.
Tafiya Mina da kwana a can. Alhazan za su gudanar da sallolin Azahar, La'asar, Magariba, Isha'i, da kuma sallar Asuba ta ranar tara ga wata a Muna, inda daga nan kuma za su tafi filin Arfa
Sai dai alhazan wasu ƙasashen sukan tafi filin Arfa tun cikin dare, ma’ana su wayi garin ranar tara ga watan na Zul hijja a can.
Sauran muhimman ayyukan Hajji
Fita Mina a ranar takwas ga watan Zul Hijja tamkar shiri ne na jiki da na ruhi yayin da mahajjata za su shiga ayyukan ibadar hajji a tsawon kwanaki biyar ko shida ka’in-da-na’in.
A kwanakin da za su biyo baya, alhazai za su gudanar da wasu muhimman ayyukan ibada kamar haka.
Tsayuwar Arfa: A ranar tara ga wata ne alhazai za su nufi filin Arfa daga Muna, inda za su wuni a can suna gudanar da ayyukan ibada. A nan ne liman zai yi hudubar Hajji, kamar yadda Annabi Muhammad SAW ya yi. Alhazai za su haɗa sallar azahar da la’asar. Tsayuwar Arfa ita ce mafi muhimmancin ayyukan aikin Hajji, wacce idan mutum bai same ta ba to bashi da aikin hajji, sai ya sake.
Kwana a Muzdalifa: Daga Filin Arfa alhazai za su kama hanya zuwa filin Muzdalifa bayan faɗuwar rana, inda za su yi sallar Magariba da Issha kuma su kwana a filin. Sai dai an yi wa wasu mutanen rangwamen cewa ba lallai sai sun kwana a Muzdalifa ba.
Ranar Sallah: Ranar 10 ga Zul hijja, wato Ranar Sallah ita ce ranar da alhazai suka fi gudanar da ayyukan ibadar hajji mafi yawa. Muhimman ayyukan sun kunshi, jifa na ranar sallah, da yanka dabbar hadaya, da Dawafi, da Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa da kuma yin aski.
Kwanakin zaman Mina: Bayan alhazai sun kammala ayyukan ranar sallah, za su koma Muna inda za su yi kwanaki biyu ko uku suna ambaton Allah.
Shirye-shiryen karbar mahajjata a Mina
Gwamnatin ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa ɗaukacin tantunan da ke birnin Muna, wadanda aka ƙera su da kayan da ba sa cin wuta, suna cikin shirin ko-ta-kwana domin saukar da miliyoyin bakin Allah.
Haka kuma, hukumomin sun tanadi dubban jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya da muhimman abubuwan buƙata, domin gudanar da aikin na ibada ba tare da wata matsala ba.
















