Wani masoyin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ɗan ƙasar Uganda ya sanar da kulob ɗin a hukumance game da niyyarsa ta ɗaukar matakin shari’a, yana mai tuhumar ƙungiyar da sakaci a aiki da rashin ƙwarewa a dabarun aiki da kuma haddasa masa damuwar zuciya.
A wata wasiƙa mai taken “Sanarwar niyyar shigar da ƙara” wadda aka rubuta ranar 11 ga watan Afrilu kuma aka rubuta adireshin hedikwatar Arsenal ta Highbury House a Landan kanta, Eric Kyama ya ce irin wasan da kulob ɗin ya yi ranar Asabar a karawarsa da AFC Bournemouth daidai yake da wani “tsagwaran ƙeta abin da za a iya kira yarjejeniyar da ke tsakanin kulob ɗin da magoya bayansa na duniya”.
Wasiƙar, wadda Kyama ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X kuma wanda wasu kafafan wasa labaran duniya suka kwafa, ta lissafa jerin wasu tuhume-tuhme kan kulob ɗin da ‘yanwasanta da kuma kocinta Mikel Arteta.
Kyama ya zargi ‘yanwasan da sakaci wajen aiki, yana mai zargin cewa sun nuna “tsabagen rashin aiki tuƙuru” kuma sun gaza nuna karsashi ko kuma saka jiki a kan fili.
‘Damuwa ta zuciya da ta kuɗi’
Ya kuma soki Arteta, yana mai iƙirarin cewa kocin ya rasa ƙwarewa na iya jagorantar ƙungiyar da kuma siffanta salon wasan kulob ɗin a matsayin abu “mai rarrabuwa” da kuma “mara alƙibla”.
Masoyin kulob ɗin ya ƙara da cewa yanayin yadda Arsenal ta yi wasan ya haddasa damuwa ta zuciya da ta kuɗi, yana mai cewa magoya bayan kulob ɗin suna zuba jarin lokaci da kuɗi da ƙuzari na zuciya cikin goyon bayan kulob ɗin.
Kyama ya kuma yi zargin rashin bayyana gaskiya a ɗabi’un kulob ɗin, yana mai cewa yadda kulob ɗin yake tallan manufofi kamar su inganci da “nasara ta hanyar haɗin kai” ya ci karo da abin da ya kira rashin nuna zafin nama a wasan.
Ya yi gargaɗin cewa idan kulob ɗin bai ba da bayani a hukuamnce ba tare da bayyana yadda zai mayar da kansa mataki na gogayya, shi zai ɗauki matakin shari’a na neman diyya bisa ga tasiri kan hankali da rasa aminci a kan kulob ɗin.








