| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Za a cim ma yarjejeniyar bututun gas na Nijeriya-Maroko kan biliyan $25 a bana: Jami'i
A bana za a saka hannu kan yarjejeniyar gwamnatocin don shimfiɗa bututun gas daga Nijeriya zuwa Maroko kan dala biliyan $25, a cewar shugaban hukumar makamashi haƙar ma'adanai na Maroko ranar Litinin.
Za a cim ma yarjejeniyar bututun gas na Nijeriya-Maroko kan biliyan $25 a bana: Jami'i
Nijeriya da Maroko sun ce aikin bututun iskar gas nasu na haɗin gwiwa zai sauya fasalin samar da makamashi ga Afirka da Turai. / Reuters
10 awanni baya

Babban jami'in hukumar albarkatun mai da haƙar ma'adanai ta Maroko (ONHYM) ya faɗa ranar Litinin, cewa za a sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin gwamnatoci (IGA) a wannan shekara, kan bututun iskar gas na Najeriya-Maroko mai kimar dala biliyan 25.

Tun shekaru goma da suka gabata aka amince da aikin wanda ake kira African Atlantic Gas Pipeline, wanda zai bi nisan kilomita 6,900 a haɗakar hanyoyin tekun da na ƙasa, tare da iyakar ƙarfin mita kubik biliyan 30, ciki har da 15 bcm don samar wa Maroko, da na fitarwa zuwa Turai, in ji Amina Benkhadra ta ONHYM a imel da ta aiko wa Reuters.

Shirin gina bututun, wanda Ƙungiyar Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ke goyon baya, an samu kammala nazarin yiwuwar aikin da matakan farko na tsara aikin injiniyancinsa.

Benkhadra ta ce, bayan sanya hannun yarjejeniyar tsakanin gwamnatocin, za a kafa wata babbar hukuma a Nijeriya don aikin bututun, wadda za ta haɗa wakilan ministoci daga kowace daga cikin ƙasashe 13 masu ruwa-da-tsaki domin samar da daidaiton siyasa da na dokoki.

Haɗin-kan tattalin arziki

Ta ce za a ƙirƙiri kamfanin aikin a Maroko a matsayin na haɗin-gwiwar kasuwanci tsakanin ONHYM da Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC), don jagorantar aiwatarwa, samar da kuɗaɗe da matakin gini.

Ta ƙara da cewa, bututun zai ƙara haɗin-kan tattalin arziƙi a faɗin Yammacin Afirka, ta hanyar faɗaɗa samar da wutar lantarki da sauƙaƙa cigaban masana'antu da haƙar ma'adanai, yayin da kuma zai taimaka wa Maroko ta samu matsayi na gadar makamashi tsakanin Afirka da Turai.

Sassan farko na aikin za su haɗa Maroko da filayen iskar gas a Mauritania da Senegal, da kuma haɗa Ghana da Ivory Coast a kudanci, kafin sashen ƙarshe ya haɗa Ghana da filayen gas na Nijeriya, in ji ta.

Ana sa ran samun iskar gas na farko daga matakan farko a shekarar 2031, in ji Benkhadra.

Aikin yana janyo hankula

Benkhadra ta ce, 'Aikin ba ya dogara ga yanke shawarar zuba-jari guda ɗaya ta duniya, kuma an tsara kowane sashe na shirin don a iya haɓakawa a matsayin 'tsari mai zaman kansa' domin ba da damar gina ƙima tun daga farko.

Ta kuma ce ba a samu ƙaddamar da kammalallen alƙawuran samar da kuɗaɗe ba tukuna, saboda tsarin haɗa kuɗaɗen zai kasance ƙarƙashin jagorancin kamfanonin aikin, wanda zai tara haɗakar jari da bashi.

'Aikin na jawo babbar sha'awa [daga fannoni daban-daban] saboda girman sa, da tsarin matakai, da matsayin dabarun da yake da shi,' in ji Benkhadra.