Tana ƙasa tana dabo game da yiwuwar babban taron Jam’iyyar adawa ta Nijeriya ADC da aka shirya yi a Abuja, babban birnin ƙasar ranar Talata inda mai wurin da za a yi taron ya janye damar da ya bai wa jam’iyyar.
Mai cibiyar taro ta Rainbow Event Centre da ke Abuja, inda ADC ta shirya yin babban taronta na ƙasa ya shaida wa jam’iyyar cewa ya janye damar ne saboda matsin lamba da ya fuskanta daga ministan birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, in ji kakakin jam’iyyar ADC Bolaji Abdullahi a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.
Abdullahi ya ce mai wurin ya shaida wa jam’iyyar cewa ministan ya yi barazanar ƙwace lasisinsa a kan taron.
“Amma mun riga mun sanya hannu a kwantiragi tare da shi. Za mu yi taronmu kamar yadda aka shirya a cibiyar taro ta Rainbow,” in ji Abdullahi.
Sai dai kawo yanzu ministan na Abuja ko kuma gwamnatin tarayyar ƙasar ba su yi tsokaci game da wannan zargin ba.
Rasa damar taro a dandalin Eagles Square
Jam’iyyar adawar ta ADC ta ɗauki matakin hayar wurin taro na Rainbow ne bayan ta yi iƙirarin cewa an hana ta amfani da dandalin taro na Eagle Square, inda ake gudanar da galibin manyan tarurkan siyasa a babban birnin ƙasar Abuja.
Jaridar Premium Times ta ambato shugaban kwamitin watsa labarai na babban taron jam’iyyar ta ADC, Kola Ologbondiyan, yana cewa jam’iyyar ta karɓi hayan cibiyar Rainbow ne saboda ba ta samu martani ba game da takardun neman izinin amfani da dandalin Eagle Square da filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja da ta rubuta wa ma’aikatar da ke gudanar da mulkin Abuja.

Sai dai ministan ma’aikatar Abuja, Nyesom Wike ya bayyana ranar Litinin cewa bai samu wata takardar neman izinin amfani da wuraren biyu ba.
“A daidai lokacin da muke magana a yanzu, babu wata takardar neman izini da aka miƙa wa ofishina ko kuma wata hukuma game da amfani da dandalin Eagle Square,” kamar yadda Wike ya bayyana yayin da yake sa ido kan ayyuka a babban birnin ƙasar.
“Wa ya hana su? Ba ni da masaniya game da wannan, kuma ban san wace jam’iyya kake magana a kai ba. Idan ADC ce, wannan irin iƙirarin da suka saba yi ne domin neman jama’a su ji tausayinsu.”
“Shaƙe dimokuraɗiyya”
Sai dai jiga-jigan jam’iyyar ta ADC sun fara yin Allah wadai da wannan matakin da suka zargi gwamnatin tarayya ta ɗauka ta hannun ministan Abuja.
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya kuma mataki na matsorata da ke amfani da ƙarfin mulki ta yadda bai dace ba.
“Bari na bayyana ba tare da wata-wata ba: tilasta wa kamfanoni masu zaman kansu su hana jam’iyyar adawa da ta yi rajista bisa doka amfani da wurinsa ba mulki ba ne. Ba siyasa ba ce, “ kamar yadda Atiku ya bayyana wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.
“ Wannan ɗabi’a ce ƙarara ta wata gwamnati da ta sha kaye a jayayya, wadda ta rasa [goyon bayan] mutane,” in ji shi.
“ADC ta biya dukkan kuɗin haya. ADC ta sanya hannu a kan ko wane kwantiragi. ADC ba ta karya ko wace doka ba. Laifinmu kawai shi ne muna shirya [kanmu], muna haɓaka, kuma muna ƙoƙarin yi wa wannan gwamnatin da ta gaza ritaya ta akwatin zaɓe a shekarar 2027,” in ji Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa da irin wannan matakin ne ake shaƙe dimokuraɗiyya.
“Ba za mu tsorata ba. Ba za mu yarda a hana mu magana ba. Ba za mu miƙa wuya ba ga wannan danniya da ke shigowa sannu a hankali, kuma ba za mu taɓa miƙa wuya ba ga ƙananan azzaluman da ke bayanta,” in ji tsohon mataimakin shugaban ƙasar














