Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bai wa ma’aikatanta da ba na gaggawa ba da iyalansu umarnin ficewa daga ofishin jakadancinta da ke Abuja, babban birnin Nijeriya saboda taɓarɓarewar tsaro a faɗin ƙasar.
A wasu jerin shawarwari da ta fitar ga Amurkawa ranar Laraba, ma’aikatar ta bayyana cewa, daga ranar 8 ga watan Afrilun shekarar 2026, an umarce su da su guji yin balaguro zuwa Nijeriya saboda yawaitar aikata laifuka da ta’addanci da garkuwa da mutane da kuma rashin zaman lafiya.
Sanarwar ta ayyana gaɓa ɗaya balaguro zuwa Nijeriya a “mataki na 3: taka-tsantsan,” yayin da wasu jihohi suke a ”matakin 4: kada ku tafi.”
Ma’aikatar ta ƙara jihohin Filato da Jigawa da Kwara da Neja da Taraba cikin jerin wurare na “kada ka tafi,” lamarin da ya sa jumullar jihohin da aka matuƙar hana zuwa ta kai 23.
“Ranar 8 ga watan Afrilu na shekarar, ma’aikatar harkokin wajen ta bai wa ma’aikatan Amurka waɗanda ba na gaggawa ba damar barin ofishin jakadancin Amurka na Abuja saboda taɓarɓarewar lamarin tsaro,” in ji sanarwar.

“Ku sake tunani game da yin balaguro zuwa Nijeriya saboda laifuka da ta’addanci da rashin zaman lafiya da garkuwa da mutane da kuma rashin tabbacin samuwar kiwon lafiya. Wasu wurare suna da ƙarin hatsari,” in ji ta.
Mataki na 4 ya bayyana cewa an yi kira ga Amurkawa su ƙaurace wa jihohi na arewa da suka haɗa da Borno da Jigawa da Kogi da Kwara da Neja da Filato da Taraba da Yobe da kuma arewacin jihar Adamawa saboda ta’addanci da laifuka da garkuwa da mutane.
Kazalika shawarar ta lissafa jihohin Bauchi da Gombe da Kaduna da Kano da Katsina da Sokoto da kuma Zamfara inda ta yi ishara da rashin zaman lafiya da aikata laifuka da garkuwa da mutane.
“Lamarin tsaro a waɗannan jihohin ba shi da tabbas saboda rashin zaman lafiya da rikici tsakanin al’ummomi da laifuka na ‘yanbindiga ciki har da garkuwa da mutane da fashin kan titi.
“Za a iya ƙaddamar aikin tsaro don kawar da wannan barazanar ba tare da gargaɗi ba,” in ji sanarwar.
A kudu maso gabashin Nijeriya kuwa, ma’aikatar ta yi kira ga Amurkawa su ƙaurace wa jihohin Abia da Anambra da Bayelsa da Delta da Enugu da Imo da Ribas (ban da birnin Fatakwal) saboda laifuka da garkuwa da mutane da rashin zaman lafiya.
“Laifuka na da yawa a kudancin Nijeriya. Akwai babban hatsarin garkuwa da mutane da zangazanga na tashin hankali da kuma aika-aikar ‘yan daban ‘yan bindiga,” in ji sanarwar.
Shawarar ta bayyana cewa laifuka na tashin hankali ciki har da ƙwace mota da garkuwa da mutane suna ƙaruwa a yankin kuma ana ganin Amurkawa na da kuɗi inda ake yawan mayar da hankali kansu.
Ta ce hare-haren ‘yanta’adda sun kasance barazana a faɗin Nijeriya ciki har da kasuwanni da kantunan cefane da otel-otel da wuraren ibada da kuma wuraren da jama’ai ke taruwa.
Ta ƙara bayyana kiwon lafiya a Nijeriya a matsayin abu taƙaitacce kuma maras tabbas inda yawancin cibiyoyin kiwon lafiya ba su da inganci irin na Amurka da Turai.
Sai dai kuma ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta yi kira ga Amurkawa da ke tunanin tafiya zuwa Nijeriya su shiga tsarin rajistar tafiyarsu domin samun muhimman bayanai da kuma yin taka-tsantsan yayin tafiya, kana su ƙaurace wa wuraren zanga-zanga da wuraren taruwar mutane.










