Babbar Alƙaliyar Nijeriya, Kudirat Kekere-Ekun ta gargaɗi kafafen yaɗa labarai da su guji ƙarin gishiri a rahotanni ko karkatar da gaskiya, tana mai cewa hakan na iya rage amincewar jama’a ga bangaren shari’a tare da raunana dimokuraɗiyya.
Ta bayyana hakan ne a Abuja a taron shekara-shekara na ƙungiyar ‘yanjarida masu ɗaukar rahotanni daga kotuna (NAJUC).
A jawabin da aka gabatar a madadinta ta hannun Babatunde Adejumo, ta jaddada muhimmiyar rawar da ‘yanjaridar kotuna ke takawa wajen bayyana yadda shari’u ke gudana ga jama’a, tare da kira gare su da su rungumi ƙwarewa da bin ƙa’idojin aiki.
Ta bayyana ‘yanjaridar kotu a matsayin gada tsakanin kotuna da al’umma, tana mai cewa aikinsu yana da muhimmanci wajen tabbatar da amincewa da tsarin shari’a, kuma rawar da suke takawa na da alaƙa da dimokuraɗiyya.
Kekere-Ekun ta yi gargaɗin cewa rahotannin da ba su da cikakken bayani ko kuma aka ƙara musu gishiri su na iya raunana bin doka da oda. Ta ce ko da hukunci ya kasance mai inganci, ba zai yi tasiri ba sai idan jama’a sun fahimce shi yadda ya kamata.
Ta kuma amince cewa rahoton shari’a yana da sarƙaƙiya kuma ‘yanjarida na fuskantar matsin lokaci da na edita, amma ta buƙace su da su ba da fifiko ga gaskiya, cikakken bayani da adalci, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Shi ma Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Lateef Fagbemi ya yi gargaɗi ga ‘yansiyasa masu haddasa rikici, yana mai kira gare su da su bi doka.
Fagbemi ya bukaci kafafen yaɗa labarai da su guji ba wa masu rarrabuwar kai kafa, tare da ƙarfafa haɗin kai da ci gaban ƙasa.
Ya ce kafafen yaɗa labarai na taka muhimmiyar rawa wajen haɗa hukumomin zaɓe, ‘yansiyasa da masu kaɗa ƙuri’a.
A nasa jawabin maraba, shugaban NAJUC na Abuja, Kayode Lawal, ya yi kira da a gyara bangaren shari’a domin kare dimokuraɗiyya.
Ya nuna damuwa kan hukuncin kotuna masu cin karo da juna, musamman a shari’o’in siyasa, inda ya ambaci rikicin da ya shafi Jam’iyyar PDP.
Lawal ya kuma buƙaci a ƙarfafa ‘yancin kai na bangaren shari’a, ciki har da samar da kuɗaɗe masu zaman kansu, sannan ya bukaci ƙungiyar lauyoyi ta Nijeriya da ta ɗauki mataki kan lauyoyin da ke aikata rashin ɗa’a.
Ya ƙara da cewa yayin da zaɓen 2027 ke gabatowa, dole ne bangaren shari’a ya ci gaba da zama mafakar talaka tare da kiyaye amincewar jama’a.












