Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa hoton da ke yawo na wani sojanta yana fasa mutum-mutumin Yesu Almasihu (Annabi Isah) a kudancin Lebanon gaskiya ne.
A ranar Litinin ne rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa hoton da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna daya daga cikin sojojinta a kudancin Lebanon yana bugun mutum-mutumin Yesu Almasihu, sahihi ne.
Wannan ya biyo bayan kakkausan suka da aka yi a fadin duniya kan wani bidiyo da ke nuna wani soja yana amfani da injin fasa dutse (Jackhammer) wajen fasa kan mutum-mutumin Yesu Almasihu a garin Deir Siryan.
Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa lamarin ya shafi wani soja ne da ke gudanar da aiki a kudancin Lebanon. Wannan keta alfarmar ta faru ne duk da ikirarin da sojojin Isra’ila suke yi na cewa “ba su da niyyar cutar da ababen more rayuwa na farar hula, ciki har da gine-ginen addini ko alamomin addini.”
Yayin da rundunar sojin ke ikirarin cewa rundunar yanki na Arewa tana gudanar da bincike kan lamarin, ba ta bayar da wani bayani kan ko wane ne sojan ba ko kuma takamaiman matakin hukunci da za a dauka.
Kakkausar suka
Tsohuwar mambar majalisar dokokin Amurka, Marjorie Taylor Greene, ta nuna bacin ranta kan wannan labari, inda ta tambayi matsayin “babban abokin kawancenmu” wanda ke karbar biliyoyin daloli na harajin jama’a da makamai.
Ryan Grim, wani fitaccen dan jarida a Amurka, ya ce: “Sojojin Isra’ila sun kwashe shekaru biyu da rabi suna wallafa hotunan laifukan yaki da keta alfarmar al’adu ba tare da tsayawa ba.”
Shi ma fitaccen mai sharhi kan al’amuran yau da kullum kuma tsohon dan majalisa, Matt Gaetz, ya kira matakin na Isra’ila da “abin ban tsoro”.
Kafafen yada labarai na Lebanon sun bayar da rahoton barna a wani wuri na Kirista a kauyen Ain Ebel da ke gunduma daya. Rahotanni sun nuna cewa hare-haren Isra’ila sun shafi wasu wuraren addini da dama a kudancin Lebanon, ciki har da kauyen Shamaa a gundumar Tyre.
Tun daga ranar 2 ga watan Maris, hare-haren Isra’ila kan Lebanon sun kashe mutane 2,294 tare da raba mutane sama da miliyan 1 da muhallansu.
Hana shugaban addini shiga coci
A watan da ya gabata, dakarun Isra’ila sun hana babban limamin darikar Katolika (Latin Patriarch) na Kudus, Cardinal Pierbattista Pizzaballa, shiga cocin Holy Sepulchre don jagorantar addu’o’in ranar “Palm Sunday”, wanda shi ne karon farko da aka taba yin irin wannan takunkumin cikin daruruwan shekaru.
Wannan mataki ya janyo suka daga shugabannin kasashen duniya da cibiyoyin addini game da batun ’yancin yin addini.
Daga baya aka janye matakin bayan matsin lamba daga kasashen duniya, inda jami’an Isra’ila suka ba da damar ci gaba da shiga cocin, amma lamarin ya fito da yadda takaddama ke karuwa game da shiga wuraren ibada a Kudus da kuma takunkumin da Isra’ila ke sanyawa Kiristoci da Musulmai.
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Sojan Isra’ila na shan suka bayan ya lalata mutum-mutumin Yesu a Lebanon
A ranar Litinin ne rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa hoton da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna daya daga cikin sojojinta a kudancin Lebanon yana bugun mutum-mutumin Yesu Almasihu, sahihi ne.
Rumbun Labarai











