Jakadan Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya, Amir-Saeid Iravani ya ce ƙawanyar hanyar ruwa da Washington ta yi kan Tehran wani misali ne na "matakin tsangwama da ya fito ƙarara " a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, yayin da yake nuna kyakkyawar fata amma da taka-tsan-tsan cewa tattaunawar da ake yi za ta iya samar da mafita.
Da yake magana ranar Alhamis a muhawara ta hawa kujerar na ƙi kan ƙudirin MƊD game da rufe Mashigar Ruwan Hormuz, Amir Saeid Iravani ya kare hawa kujerar navƙi da China da Rasha suka yi kuma ya zargi Amurka da haddasa rikicin ta hanyar ƙarfin soji.
"Ƙaƙaba ƙawanyar hanyoyi ruwan da Amurka ta yi shelar yi wani keta ‘yancin ƙasar Iran ne mai muni," kamar yadda Iravani ya bayyana, yana mai kiransa "wani matakin tsangwama da ke bayyane a dokokin ƙasa da ƙasa."
Ya ce matakan Washington sun yi lahani ga wasu ƙasashe na daban ma, yana mai ce wa Amurka “tana keta ‘yancin gudanar da kasuwanci ta hanyar ruwa na wasu ƙasashe ma."
Iravani ya jaddada cewa Iran ta yi aiki bisa doka, yana mai cewa Tehran ta "ɗauki matakan riga kafin ne domin tabbatar da tsaro na wucewa ta Mashigar Ruwan Hormuz," matakan da "aka shirya domin taimaka wa ci-gaba da wucewar jiragen ruwa cikin aminci tare da hana amfani da hanyar ruwan domin dalilai na hamayya ko na soji."
Duk da zarge-zargen, ya yi ishara ga buƙatar diflomasiyya kuma ya ce: "Duk da rashin yarda mai zurfi da muke da shi kan Amurka, wanda ya sami asali daga yaudarar diflomasiyya da ta yi ta maimatawa, duk da haka mun shiga tattaunawa cikin kyakkyawar niyya kuma muna nan da kyakkyawan fata amman da taka-tsan-tsan."
"Mun yi imanin cewa idan Amurka ta ɗauki hanya ta hankali da kuma neman gyara kuma ta kauce wa neman wasu buƙatu da ba su dace da dokokin ƙasa da ƙasa ba, waɗannan tattaunawar za su iya samar da sakamako mai ma’ana," in ji shi.
Iravani ya kuma soki zaman kanta, yana mai nuna rashin yarda da abin da ya kira "wata magana ta son-kai da ta karkata gefe ɗaya" da shugabar taron Majasalisar Ɗinkin Duniyar Annalena Baerbock ta yi, yana mai zarginta da "kauce wa nauyin da rataya a kan kujerarta " da kuma gaza tabbatar tsantsan adalcin da aikinta ke buƙata.
Ya ƙarƙare da watsi da "dukkan zarge-zarge mara tushe da waɗanda suka samo asali daga siyasa " da aka yi kan Iran a lokacin taron.






