Ƙungiyar masu kamfanonin jiragen saman Nijeriya (AON) ta yi gargaɗin cewa jiragen sama a faɗin ƙasar za su iya dakatar da ayyuka daga ranar 20 ga watan Afrilu na shekarar 2026, bisa abin da ta bayyana a matsayin “tashin gwauron zabi ” na farashin man jirgin sama.
A wata wasiƙa da aka rubuta ranar 14 ga watan Afrilun shekarra 2026 kuma aka aika ga shugaban ƙungiyar manyan dillalan makamashi ta Nijeriya (MEMAN), Mista Clement Isong, AON ta ce farashin man jirgi ya tashi daga ₦900 kan ko wace lita a ranar 28 ga watan Fabrairu zuwa ₦3,300 kan ko wace lita a yanzu — ƙarin fiye da kashi 300 a cikin makonni kaɗan.
Ƙungiyar ta ce, tashin farashin “wani abin da aka kitsa ne” kuma ya zarce yadda abubuwa suke a duniya, tana mai cewa farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya tashi ne kawai da kashi 30 cikin 100 a cikin wannan lokacin.
‘Mai zagon ƙasa ga lafiyar ƙasa’
Ƙungiyar masu jiragen saman ta ce kamfanonin jiragen sama sun ci gaba da ɗaukar nauyin tsadar da ke ƙaruwa bisa “kishin ƙasa da kuma cikin tunanin yi wa ƙasa hidima,” amma sun yi gargaɗin cewa nauyin ba abin da za a iya ci gaba da jurewa ba ne.
“Kuɗaɗen shiga na kamfanonin jirage ba su isa ɗaukar nauyin farashin mai kaɗai ba,” a cewar wasiƙar, inda ta ƙara da cewa lamarin ya taɓarɓare zuwa wani mummunan mataki da aiki ba zai yiwu ba.
Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa matakan da dillalan man suka ɗauka suna “laƙume masana’antar sufurin sama” kuma suna barazana mai yawa ga tattalin arzikin Nijeriya da aminci da tsaron ƙasa.
Ƙungiyar AON ta bayyana cewa tasirin tashin farashin ya fara bayyana a faɗin masana’antar, tana mai cewa wani kamfanin jiragen sama ya riga ya dakatar da ayyukansa tun ranar 13 ga watan Maris na shekarar 2026, sakamakon tashin farashin man.
Ta yi gargaɗin cewa ƙarin kamfanonin jiragen sama za su iya bin sawun kamfanin idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
“Masana’antar sufurin jiragen sama wata masana’anta ce mai muhimmanci ga ƙasa,” in ji wasiƙar, tana mai gargaɗin cewa farashin mai na yanzu “ba shi da kyau kuma yana zagon ƙasa ga lafiyar ƙasa.”
Sanarwa ta ƙarshe ga dillalan mai
Ƙungiyar kamfanonin jiragen saman ta ayyana zaɓi mai wuya da ke fuskantar masana’antar: ƙara kuɗin tikitin jirgi domin nuna yadda farashin mai ke ƙaruwa zai iya rage yawan fasinjoji masu hawa jirage, yayin da dakatar da aiki gaba ɗaya zai yi tasiri mai yawa.
Sun yi gargaɗin cewa dakatar da aiki gaba ɗaya zai yi tasiri kan ma’aikatun kuɗi da katse hanyoyin samun kuɗin miliyoyin mutane tare da tsananta matsalar tsaro a faɗin ƙasar.
AON ta yi kira ga MEMAN ta sa baki kuma ta tabbatar da cewa an sauya farashi man jirgi zuwa yadda farashin mai yake a kasuwannin duniya, tana mai jaddada cewa kamfanonin jiragen sama ba za su iya ci gaba da sayan mai ba a farashin da ke akwai a halin yanzu.
“Saboda haka, muna ba da sanarwa cewa idan wannan yanayin ya ci gaba, dukkan kamfanonin jiragen sama a Nijeriya zai zama musu tilas su dakatar da ayyukansu daga ranar Litinin 20 ga watan Afrilun shekarar 2026. Wannan shi ne kiranmu na ƙarshe,” in ji wasiƙar.
Manyan jami’an gwamnati, ciki har da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, da ministan sufurin jiragen sama da hukumar jigilar fararen-hula ta sama NCAA da hukumar tsaro ta farin kaya DSS na cikin waɗanda aka tura wa kwafi na wasiƙar.
Wannan lamarin ya sanya sabuwar damuwa game da zaman lafiya a masana’antar sufurin jiragen saman Nijeriya, yayin da masu ruwa da tsaki ke jiran martani daga dillallan man da hukumomin gwamnati cikin kwanaki masu zuwa.









