Dakarun sojin Nijeriya sun zafafa kai samame a sansanin 'yanta'addan IPOB’ESN a faɗin kudu maso gabashin ƙasar inda suka lalata maɓoyar tare da ƙwace makamai.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinta na X ranar 15 ga watan Afrilu ta ce wani samame da dakarun runduna ta musamman ta Operation Eastern Sanity suka kai dajin Ajali, a ƙaramar hukumar Ezeagu ta jihar Enugu ranar 14 ga watan Afrilu ya tilasta wa ‘yanta’addan IPOB/ESN tserewa inda suka bar kayayyakinsu ciki har da nakiyar tarwatsa tankokin yaƙi.
“Tawagar jami’an tsaro ta kawar da abubuwa masu fashewa da ta samu a wurin, inda ta hana yiwuwar yin lahani ga dakaru da fararen-hula,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa dakarun sun lalata sansanonin da mayaƙan ke ɓuya ta yadda ba za su iya sake haɗuwa a wuraren ko kuma su samu wata kariya a wuraren ba.
A wani samame makamancin hakan a ranar Talatan, dakarun da aka tura Adani a ƙaramar hukumar Uzo-Uwani, da suke aiki bisa bayanan sirrin da suka samu daga jami’an tsaro na farin kaya DSS, sun bi sawu tare da kama wani kuɗin fansa da ke da alaƙa da wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane.

“Samamen ya sa an kama wani ƙasurgumin wanda ake zargi da garkuwa da mutane, lamarin da ya sake bayyana yadda ƙungiyar ke dogaro kan aikata laifuka wajen ɗaukar nauyin gudanar da ita,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa bincike a wurin ya sa an samu wata bindiga da kuma kuɗi da ya kai naira miliyan biyu (₦2,000,000), wanda aka yi imanin cewa kuɗin fansa ne daga gidan wanda ake zargin.
“Wanda ake zargin da abubuwan da aka ƙwacen an miƙa su ne ga hukumomin da suka dace domin cikakken bincike domin gano sauran ‘yan ƙungiyar masu aikata laifukan,” in ji sojin.
Ta ƙara da cewa wannan aikin ya ƙara kassara ikon IPOB/ESN na aika-aika ko na kudi, wanda ya nuna cewa ƙungiyar tana rasa tagomashi a ƙarƙashin matsi na soji, in ji sanarwar.
Ta jaddada cewa sojin za ta ci gaba da matsa wa masu aikata laifuka da kuma hana su wuraren ɓuya a fadin yankin.













