| Hausa
NIJERIYA
4 minti karatu
NBC ta yi barazanar hukunta kafafen yaɗa labaran da suke saɓa ƙa’idojin aikin jarida a Nijeriya
Wannan ya biyo bayan abin da ta bayyana a matsayin ci gaba da samun saɓa wa ka’idojin aiki, musamman a bangaren labarai, lamuran yau da kullum, da shirye-shiryen siyasa.
NBC ta yi barazanar hukunta kafafen yaɗa labaran da suke saɓa ƙa’idojin aikin jarida a Nijeriya
NBC ta yi barazanar hukunta kafafen yaɗa labaran da suke saɓa ƙa’idojin aikin jarida a Nijeriya / Nigerian Government

Hukumar NBC ta koka kan yadda ake yin watsi da ƙwarewar aiki, amfani kafafen yada labarai ta hanyar da ba ta dace ba da ’yansiyasa ke yi, da kuma ƙaruwar kalaman nuna ƙiyayya, inda ta cewa za ta sanya takunkumi ga gidajen yada labaran da suka saɓa wa ƙa’ida.

Hukumar Kula da Kafofin Yada Labarai a Nijeriya, NBC ta fitar da sanarwar gargadi ga gidajen yada labarai a fadin kasar, inda ta yi gargadin daukar matakai masu tsanani wajen tabbatar da bin ka’idojin aikin jarida na Nijeriya (Nigeria Broadcasting Code).

Wannan ya biyo bayan abin da ta bayyana a matsayin ci gaba da samun saɓa wa ka’idojin aiki, musamman a bangaren labarai, lamuran yau da kullum, da shirye-shiryen siyasa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Jumma’a, hukumar ta ce ta kula da wani tsari mai ta da hankali inda ake kara amfani da kafafen yada labarai ta hanyoyin da ke gurgunta babban nauyin da ke kansu na sanar da jama’a gaskiya tare da “daidaito, adalci, da kwarewa.”

Hukumar ta ce wannan dabi’a, idan ba a dakatar da ita ba, tana iya haddasa raguwar amincewar da jama’a ke yi wa kafafen yada labarai, sannan ta kara rura wutar dambarwa yayin da kasar ke kara kusantar babban zaben shekarar 2027.

Daukar tsauraran matakai

NBC ta jaddada cewa za ta tabbatar da “tsauraran matakai ba tare da sassauci ba” wajen bin tanade-tanaden bugu na shida (6th Edition) na kundin ka’idojin yada labarai na Nijeriya.

Ta bayyana wasu fannoni na musamman da suka hada da adalci, gaskiya, daidaito, gujewa kalaman kiyayya, da kuma girmama hukumomin hukumomin kasar, tana mai gargadin cewa saba wa wadannan fannoni zai sa a hukunta kafar yada labaran da ta yi hakan.

“Yayin da muke kusantar babban zaben 2027, hukumar tana sanar da dukkan masu yada labarai da masu ruwa da tsaki cewa za ta tabbatar da tsauraran matakai ba tare da sassauci ba kan kowane tanadi na kundin ka’idojin yada labarai na Nijeriya, musamman wadanda suka shafi adalci, daidaito, gaskiya, kalaman nuna kiyayya, tunzuri jama’a, da girmama hukumomin kasar,” in ji hukumar.

Daya daga cikin manyan matsalolin da hukumar ta nuna damuwa akai shi ne abin da ta kira ” rashin kwarewa” a tsakanin masu gabatar da shirye-shirye.

A cewar NBC, an lura da kaucewa daga matsayin aikin jarida da aka sani, ciki har da yanayin da masu gabatarwa ke hadawa da ra’ayoyinsu na kashin kai a cikin shirye-shirye, ko rashin bai wa bangarorin adawa damar fadin albarkacin bakinsu, ko barin tattaunawa ta karkata zuwa ga goyon bayan wasu bukatun kashin kai.

Irin wadannan ayyuka, in ji hukumar, sun saba wa bayyanannun tanade-tanade na kundin ka’idojin yada labarai wadanda ke bukatar nuna matsayi tsaka-tsaki da adalci wajen tafiyar da al’amuran da suka shafi moriyar jama’a.

Sukar matakin

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya soki gargaɗin da Hukumar NBC ta yi, inda ya bayyana hakan a matsayin wani yunƙuri na dakile ’yancin kafafen yaɗa labarai da kuma taƙaita fadin albarkacin baki a kasar.

Shi ma wani fitaccen dan jarida wanda yake aiki da kafar yada labarai ta Arise News Oseni Rufai ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da matakin da NBC take shirin dauka a kasar.

Kuma ya zargi hukumar da saɓa wa kundin tsarin mulkin kasar, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X.

Kungiyar Kare Hakkin Dan’adam ta Amnesty International ta yi Allah wadai da kakkausar murya game da gargadin da hukumar NBS ta yi na toshe bakin ’yanjarida da kafafen yada labarai, ta hanyar wata ‘sanarwa ta hukuma ga masu yada labarai’, wacce take saba wa doka.

Kungiyar ta ce hukumar ba ta da ikon sanya doka ko ikon fada wa ’yan jarida yadda za su gudanar da aikinsu.

A cewar Amnesty International sanarwar NBC ta karkata ga shirye-shiryen siyasa da masu gabatar da shirye-shiryen al’amuran yau da kullum, ta sanya takunkumi mai tsauri da katsalandan ga kafafen yada labarai da ’yan jarida.

Kazalika ta ce NBC tana so ne ta matsa wa ’yanjarida da kafofin yada labarai lamba domin su rika tace kansu (da kansu) saboda tsoro.

Rumbun Labarai
‘Yan Nijeriya fiye da 67,000 sun amfana da shirin ba da lamuni ga ƙananan masana'antu – Tinubu
Tinubu yana nan lafiya, zai koma Nijeriya a makon nan: Fadar Shugaban ƙasa
Kwalara ta kashe wasu fursunoni a gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Kano
Sojojin Nijeriya sun kama mutum uku da ake zargi da yi wa ‘yanta’adda aikin masinja a Katsina
An sake harbe wani ɗan Nijeriya har lahira a Afirka ta Kudu
Nijeriya ta buƙaci a bai wa Afirka kujeru biyu na dindindin a Kwamitin Tsaro na MƊD
Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar biliyan $700 a ɓangaren haƙar ma'adinai
Ƙungiyar Amnesty International ta soki gwamnatin jihar Kano a Nijeriya kan musguna wa ‘yan adawa
Ba na da-na-sanin taimaka wa waɗanda suka yi watsi da ni a yanzu— El-Rufai
Tsaro a Arewa maso Yammacin Nijeriya: Me ke bayan raguwar kashe-kashe, me ke ƙara tayar da hankali?
Kalaman Malami da Fagbemi sun ci karo da juna kan yarjejeniyar sulhu ta $200m kan aikin Mambila
Gwamnatin Nijeriya ta bayar da wa’adin mako biyu don bincike kan mutuwar mutum 37 a hannun NSCDC
Ana zargin wasu ’yan siyasar Nijeriya da karkatar da $271m na gwamnati sun sayi gidaje a Amurka
An gudanar da zanga-zangar neman a kubutar da daruruwan mutane da aka yi garkuwa da su a jihar Neja
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce Shettima na da cikakken ikon wakiltar Tinubu a taron UNGA
Matsalar haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a Nijeriya
'Yanbindiga sun kashe mutum tara a jihar Filaton Nijeriya
An kama mai PoS da ake zargi da aiki da taimakon mai garkuwa da mutane
An tsare kwamandan NSCDC da wasu jami'an hukumar na jihar Neja kan mutuwar masu haƙar ma'adinai 37
Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamitin mutum 10 don binciken mutuwar mutum 37 a hannun NSCDC a Neja