‘Yan bindiga sun kai hari kan wata motar bas ɗin fasinjoji a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya a ranar Alhamis, sun sace wasu ɗalibai yayin da suke kan hanyarsu zuwa zana jarrabawar shiga jami'a ta JAMB, in ji jami'ai.
An sace ɗaliban da sauran fasinjoji a kan hanyar Otukpo–Makurdi, in ji Hyacinth Alia, gwamnan Benue, a cikin wata sanarwa.
Gwamnan bai fayyace adadin wadanda aka ɗauka ba, amma kafafen watsa labaran cikin gida sun ce adadin fasinjojin da ke cikin motar shi ne 14.
"Kai hari ga fararen hula da ba su ji ba, ba su gani ba, musamman ɗalibai da ke kan hanyarsu zuwa jarabawa, ba abin yarda ba ne kuma ya saba wa kowace al'ada ta ɗan adam da tsarin zaman lafiya," in ji Alia.
Bincike da ceto
A halin yanzu ana gudanar da ayyukan bincike da ceto don tabbatar da dawowar duk wadanda aka sace cikin koshin lafiya, in ji gwamnan.
Babu wata kungiya da ta ɗauki alhakin sace-sacen da suka faru a ranar Alhamis.
Gwamnan Benue ya yi kira ga mazauna su kasance cikin natsuwa tare da ci gaba da yin haɗin gwiwa da jami'an tsaro wajen ƙoƙarin ceto da sauran ayyuka.
"Za mu ci gaba da ɗaukar matakai masu ƙarfi don kare rayuka da dukiyoyi," in ji shi.








