| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Isra’ila tana amfani da batun tsaro wajen ƙwace ƙarin filaye – Ministan Harkokin Wajen Turkiyya
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana cewa Isra’ila tana amfani da batun tsaro a matsayin hujja na neman mallakar “ƙarin wurare.”
Isra’ila tana amfani da batun tsaro wajen ƙwace ƙarin filaye – Ministan Harkokin Wajen Turkiyya
Hakan Fidan ya ceIsra’ila tana amfani da batun tsaro wajen ƙwace ƙarin filaye / AA

Babban jami’in diflomasiyyar Turkiyya ya bayyana cewa Isra’ila na ci gaba da shirin “faɗaɗa mamaya” daga yankunan Falasɗinu zuwa ƙasashen Lebanon da Siriya.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana cewa Isra’ila tana amfani da batun tsaro a matsayin hujja na neman mallakar “ƙarin wurare.”

“Isra’ila ba tsaron kanta take nema ba. Isra’ila tana neman ƙarin filaye ne. Gwamnatin Netanyahu tana amfani da batun tsaro ne kawai a matsayin hanzari na mamaye ƙarin ƙasa,” in ji Fidan a wajen taron dandalin diflomasiyya na Antalya (Antalya Diplomacy Forum) a ranar Asabar.

Fidan ya ci gaba da cewa, “Isra’ila ta gina wani tunani na daban a idon duniya, tana ikirarin cewa tana goyon bayan tsaron kanta ne, amma abin ya fito fili, musamman a shekarun baya-bayan nan... lamarin ya wuce haka.”

Ya bayyana cewa matakan da Isra’ila ke ɗauka tun daga yankunan Falasɗinu, Gaza, Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, Kudancin Kudus, sannan yanzu ta nufi Lebanon da Siriya, “shiri ne na ci gaba da mamaya da faɗaɗa iko a yankin.”

“Ina jin ya kamata a dakatar da wannan,” in ji Fidan.

“Dole ne Isra’ila ta sani cewa hanya ɗaya tilo da za ta iya zama cikin zaman lafiya a yankin... ita ce ta bar sauran ƙasashe su mori nasu zaman lafiyar, da ’yancin mallakar ƙasarsu, da kuma cin gashin kansu, maimakon yin amfani da ƙarfin soja a kan waɗannan ƙasashe,” in ji shi.

Shugabannin duniya da manyan jami’an gwamnati ne suka taru a Turkiyya tun daga ranar Juma’a har zuwa ranar Lahadi domin taron diflomasiyya na Antalya — wani babban taro na ƙasa da ƙasa a birnin da ke gaɓar tekun Mediterranean, wanda a wannan shekarar ya mayar da hankali kan yadda za a magance rashin tabbas a duniya.

Taron, wanda ake gudanarwa a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan kuma Ma’aikatar Harkokin Waje ta karɓi baƙunci, zai tattauna ne a kan taken “Zana Taswirar Gobe, da Shawo Kan Rashin Tabbas.”

Rumbun Labarai
An fara baje-kolin kayan tsaro da sufurin sararin samaniya na SAHA 2026 a Istanbul
Turkiyya ta zargi Isra’ila da yin 'fashi a teku' bayan tare jirgin ruwan agaji na Gaza
Turkiyya ta yi kira ga ƙasashen Musulmai da su haɗa kai wajen ba da labarinsu da kansu
Tsarabar Antalya: Turai na iya yin biris da Turkiyya amma hakan na iya rusa ta
Turkiyya ta hana yara ‘yan ƙasa da shekara 15 amfani da kafafen sada zumunta
An fara Taron Diflomasiyya na Antalya na 2026 inda shugabannin duniya ke halarta
Shugaban majalisar dokokin Turkiyya ya yi kira da a dakatar da Isra'ila daga MDD
Shugabannin duniya za su hallara a Turkiyya domin taron diflomasiyya na Antalya karo na 5
Abubuwan da suka kamata ku sani game da jirgin ruwan hakar mai na Cagri bey da ya isa Somalia
Erdogan ya gaya wa Pezeshkian cewa tattaunawar Amurka da Iran za ta samar da zaman lafiya mai ɗorewa
Yadda Ma'aikatar Tsaro ta Turkiyya take taimakawa wajen rage tunzurin yanki ta bayan fage
An kawar 'yanta'adda 3 kusa ta ofishin jakadancin Isra'ila a Istanbul: Ministan Cikin Gidan Turkiyya
Turkiyya ta ƙaddamar da shirin jigilar kaya ta Saudiyya saboda rufe Mashigar Hormuz
Israila na ci gaba da kawo cikas ga duk wani ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Iran: Erdogan na Turkiya
'Masu gurɓataccen ra'ayi': Me ya sa ƙaruwar gudunmawar Turkiyya a NATO ke kaɗa hantar Isra'ila?
Ruwa na maye gurbin mai a matsayin arziki mafi muhimmanci: Erdogan na Turkiyya
Turkiya ta doke Kosovo inda ta samu damar shiga gasar cin kofin duniya ta 2026
Zero Waste: Ƙarƙashin jagorancin Emine Erdogan, duniya ta tuna da Ranar Kawar da Shara
Shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta Turkiyya ya yi gargaɗi kan rikicin Iran na iya zama na duniya
Kare gaskiya na da matuƙar muhimmanci a 'zamanin labaran ƙarya': Daraktan Sadarwa na Turkiyya