A karo na biyar, Turkiyya ta karbi bakuncin taron diflomasiyya na Antalya, inda ta sake samar da wani dandali na diflomasiyya na duniya - inda aka tattauna daga Gaza da Iran zuwa Ukraine.
Yayin da ake samun wakilci a tsakanin kasashen duniya, Yammacin Turai ya kasance a gefe guda.
Wannan ya fi ban mamaki ganin cewa Turai ta fi fama da rikice-rikicen da ake fama da su a yanzu - daga yakin Ukraine da kuma karuwar matsalar tsaro a Gabas ta Tsakiya zuwa rashin tsaro a fannin makamashi.
Maimakon amfani da wannan matakin na diflomasiyya, Turai ta ci gaba da kasancewa a ware, sakamakon shakku a akida da kuma sauyin da aka samu a dangantakar karfin iko ta duniya.
Sakamakon haka, rawar da Turkiyya ta taka a matsayinta na mai zaman kanta a fannin diflomasiyya na kara bayyana.
Habakar rawar diflomasiyya ta Turkiyya
A ‘yan shekarun nan, Turkiyya ta zama babbar mai taka rawa ta hanyar amfani da diflomasiyya da karfin kayan tsaro.
Idan aka yi duba ga manyan batutuwan da suka mamaye fagen kasa da kasa, a bayyane yake karara cewa da yawa daga wadannan rikice-rikice na afkuwa a yankunan da Turkiyya take.
Boren Kasashen Larabawa ya kai ga yakin basasar Syria a kan iyakar kudancin Turkiyya, yayin da tuni yakin Iraki ya riga ya kawo cikas ga yankin.
A arewa, yakin Rasha da Ukraine ya ci gaba, yayin da a gabas, mamayar Armenia na tsawon shekaru da dama a Nagorno-Karabakh ta ƙare tare da warware rikicin da ke tsakanin Azerbaijan da Armenia.
Yaƙin basasa a Libya ma ya girgiza yankin Bahar Rum kuma yana da tasirin tsaro kai tsaye ga Turkiyya.
Tun daga ranar 7 ga Oktoban 2023, yanayin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya ya ƙara taɓarɓarewa. Ɗaya daga cikin mafi munin laifuka a tarihin baya-bayan nan ana aikata su ne ga Falasdinawa a Gaza.
A lokaci guda, Isra'ila ta faɗaɗa ayyukanta na soji a yankuna daban-daban.
Tare da hare-haren haɗin gwiwa na Amurka da Isra'ila kan Iran da suka fara a ranar 28 ga Fabrairu, rikicin ya kai wani sabon mataki inda duniya ke girban sakamakon - misali, a rufe mashigar Hormuz da kuma ƙara taɓarɓarewar matsalar makamashi.
Duk waɗannan rikice-rikicen na faruwa ne a cikin yankunan da ke da muhimmnaci ga Turkiyya kuma suna shafar tsaro, tattalin arziki, da kuma damuwar jinkai kai tsaye a ƙasar.
Ankara ta taka rawa mai ƙarfi da kuma yin tasiri a wannan yanayi. A wasu lokuta, Turkiyya ta shiga tsakani ta hanyar amfani da ayyukan soji. Misali, a Syria, Libya, da kuma a yankin Nagorno-Karabakh.
A wasu yanayin, ƙasar ta yi aiki a matsayin mai shiga tsakani, musamman tsakanin Rasha da Ukraine - ko dai wajen warware matsalar hatsi, sauƙaƙe musayar fursunoni, ko kuma sauƙaƙe tattaunawa kai tsaye tsakanin ɓangarorin da ke rikici.
Ƙarfafa ƙarfin soja da diflomasiyya na Turkiyya ya taimaka wajen shawo kan wasu rikice-rikice, kuma a wasu lokutan, hana ci gaba da faɗaɗar rikicin.
Waɗannan cigaban sun mayar da Turkiyya daga ƙasar da ta daɗe tana fama da ƙalubalen cikin gida zuwa muhimmiyar mai taka rawa a yankin da kuma zama mai karfi a duniyar da ke tasowa.
A yau, Turkiyya ba wai kawai wani ɓangare ne na yanayin da ake rikici a cikin sa ba, a’a ta zama wata mai yin tasiri sosai a kansa..
A wannan yanayin, ana iya fahimtar Taron Diflomasiyya na Antalya a matsayin wata alama ta ƙwarewar diflomasiyya mai ƙarfi, ƙarfinta na siyasa don ɗaukar mataki, da kuma alaƙarta da sauran masu ruwa da tsaki na ƙasashen duniya daban-daban.
A cikin yankunan da aka ambata a rikicin, Turkiyya ta ɗauki matsayi wanda ya bambanta sosai da na ƙasashen Yammacin Turai da yawa.
Yayin da yawancin ƙasashen Yammacin Turai suka daidaita manufofinsu da na Isra'ila, Ankara ta nemi ta mayar da kanta ga turbar dokokin ƙasa da ƙasa da al'adun diflomasiyya da aka samar.
Wannan gamayya ta manufofin ƙasashen waje masu ƙa'ida, sassaucin dabaru, da gogewar diflomasiyya ne ya bai wa Turkiyya matsayi mai ƙarfi da aminci.
Ankara ba wai kawai ta yi amfani da wannan matsayi ne don tabbatar da 'yancin kanta na cim ma manufofinta ba, har ma ta yi amfani da shi don magance rikice-rikice.
Turkiyya ta dogara ne akan ginshiƙai uku masu muhimmanci: na farko, matsayin siyasa mai daidaito da fahimta; na biyu, ƙwarewarta ta diflomasiyya ta tarihi; na uku, ƙarfin soja da ƙarfin hana yi mata barazana.
Nasarar da aka samu a taron diflomasiyya na Antalya, wanda aka gudanar a karo na biyar a wannan shekarar, na wakiltar mafi bayyanar wannan cigaban ya zuwa yanzu.
Yawaitar manyan ƙasashen duniya da suka halarta, faɗin batutuwan da aka tattauna, da kuma yadda dandalin ya ƙara dacewa ya nuna cewa Turkiyya tna ƙara tabbatar da kanta a matsayin cibiyar diflomasiyya mai zaman kanta.
Wani wuri ne da ra'ayoyi daban-daban ke haɗuwa, kuma ana sake yin shawarwari kan rikice-rikicen duniya fiye da tsarin da aka saba gani na Yammacin duniya.
Turai a diflomasiyyar duniya: mai taka rawa ko ‘yar kallo?
Yawancin rikice-rikicen da aka ambata a sama suna shafar Turai kai tsaye. Yaƙin Rasha da Ukraine, rawar da Isra'ila ta taka wajen rushe tsarin ƙasa da ƙasa da tubalin doka, hare-haren da aka kai wa Iran, da kuma sabon rikicin makamashi da ya biyo baya yana lalata muradun ƙasashen Turai kai tsaye.
Duk da haka, bayanai game da Turai gaba ɗaya abin damuwa ne. Ko a warware waɗannan rikice-rikicen ko kuma a wajen takaita sakamakonsu yadda ya kamata, Turai ba ta sami damar yin wani abu mai zaman kansa ba.
Gaskiyar cewa nauyin siyasar Turai a teburin tattaunawa yana raguwa kuma ikonta na yin aiki yana da matuƙar iyaka ba tare da goyon bayan Amurka ba yanzu gaskiya ne a siyasar Turai.
Don kalubalantar wannan yanayin, tambayar hanyoyin da za a bi ta taso. Yin duba ga yanayin dabarun Turai yana bayyana ƙuntatawa a cikin tsarin da nahiyar ke samun kanta a ciki.
Tsintar kanta a tsakanin Rasha a matsayin ƙalubalen manufofin tsaro da China a matsayin ƙarfin tattalin arziki, Turai ta ci gaba da rasa 'yancin kai. A ƙarƙashin waɗannan yanayi, neman sabbin abokan hulɗa ya zama batu na gaggawa.
Turkiyya ta fito a matsayin zaɓi na bayyane. Kusancin ta a yankin ƙasa, ƙarfinta na siyasa, da kuma kasancewar ta a muhimman yankunan rikici suna ba wa Turai wata dama ta musamman don sake samun damar yin wani abu da suka rasa.
Saboda haka, abin mamaki ne cewa duk da waɗannan damarmaki, Turai ta ci gaba da guje wa zurfafa haɗin gwiwa da Turkiyya.
Maimakon haɓaka sabbin haɗin gwiwa da dabaru, Turkiyya tana ƙara samun haɗin kai da abokan hamayyarta na siyasa na Turai kamar Rasha da China.
Bayanan da Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta yi kwanan nan sun nuna wannan matsayin: Turai tana mayar da Turkiyya gefe a matsayin abokiyar adawa.
Ko da yake daga baya an tantance wannan magana, duk da haka yana bayyana ra'ayin Turai game da Turkiyya.
Wannan matsayi ya zama kamar yana ƙara zama mara ma'ana idan aka yi la'akari da gaskiyar yanayin ƙasa. A lokacin da rashin tabbas da raguwar tasirinsa ke ƙaruwa, nesantuwa daga Turkiyya saboda akida ba zai fahimtu ba.
Turai dole ne ta sake duba manyan manufofinta na dabaru kuma ta faɗaɗa sararinta na yin wani abu. Haɗin gwiwa da Turkiyya a kan daidaito ba zaɓi ba ne, ya zama dole.
Lokacin da za a sake fasalin wannan tsari yana da iyaka. Yayin da tsarin duniya ke ci gaba da canzawa, damar Turai ta yin sauye-sauye na ƙara raguwa.

















