| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Trump ya ce za a yi amfani da ‘manyan katafilolin tone kasa’ don kwashe sinadarin Uranium daga Iran
Sabbin kalaman na Trump a jihar Arizona sun zo ne bayan da Iran ta sha alwashin cewa ba za a taba mika ajiyayyan sinadarin “Uranium” dinta zuwa “ko’ina” ba.
Trump ya ce za a yi amfani da ‘manyan katafilolin tone kasa’ don kwashe sinadarin Uranium daga Iran
Trump / AP
5 awanni baya


Shugaba Donald Trump ya sake jaddada ikirarinsa na cewa Amurka da Iran za su hada gwiwa wajen kwashe sinadarin Uranium daga cibiyoyin nukiliyar kasar ta hanyar amfani da manyan katafilolin tone kasa (Excavators) a karkashin kowace irin yarjejeniyar zaman lafiya, kafin a kwashe kayayyakin zuwa yankin Amurka.

Kalaman na Trump na ranar Jumma’a sun zo ne duk da cewa Ma’aikatar Harkokin wajen Iran ta bayyana a baya cewa ajiyayyen sinadarin Uranium da Iran take da shi ba za a taba kai shi “ko ina” ba.

“Wani ya tambaya, ta yaya za mu kwashe wannan ɓurɓushin na nukiliya? Za mu samu ne ta hanyar shiga tare da Iran, tare da amfani da manyan injinan tone kasa masu yawa,” in ji Trump yayin da yake jawabi ga taron masu ra’ayin mazan jiya na kungiyar Turning Point USA a Phoenix, jihar Arizona.

Ya kara da cewa, “Muna bukatar manyan injinan tone kasa.”

“Amma za mu shiga tare ne da Iran. Za mu dauka. Kuma za mu dawo da shi gida Amurka nan ba da dadewa ba.”

Yarjejeniyar Lebanon da Isra’ila

Kalaman na Trump sun kara fito da karin haske kan ikirarin da ya yi a ranar Alhamis na cewa Iran ta amince ta mika sinadarin Uranium dinta, amma bai bayar da cikakken bayani kan yadda kwashewar za ta kasance ba.

Shugaban na Amurka yakan yi amfani da kalmar “nuclear dust” (barbashin Nukiliya) yana nufin ajiyayyan sinadarin Uranium din Iran, wanda Amurka ke zargin Iran da tarawa domin kera bam din Nukiliya.

Sai dai wani lokacin ma yana amfani da kalmar don nufin abubuwan da suka rage sakamakon hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin Nukiliyar Iran a watan Yunin shekarar da ta gabata.

Trump ya nuna alamun kyautata zato a ranar Juma’a game da samun yarjejeniyar zaman lafiya da Iran, inda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa “babu wata sauran matsala” kuma yarjejeniyar ana “kusa da kulla yarjejeniya.”

Ya yi wadannan kalaman ne a yayin jawabi ga kungiyar Turning Point USA, inda Erika Kirk, matar marigayi Charlie Kirk wanda ya kafa kungiyar kuma babban abokin kawancen Trump da aka kashe a watan Satumba, ta gabatar da shi.

Trump ya kuma soki kawancen soja na NATO, inda ya bayyana cewa a halin yanzu Amurka ba ta bukatar taimakonta. Haka kuma, ya yaba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Lebanon da Isra’ila, wadda ya ce “an kulla ta ne bayan shekaru 78", ya kara da cewa Amurka za ta “sake mayar da Lebanon kasa mai daraja.”