| Hausa
AFIRKA
3 minti karatu
Yaƙi ya jefa fiye da kashi 70 cikin 100 na 'yan ƙasar Sudan cikin talauci, in ji MƊD
"Shekara uku da fara rikicin, ba wani rikici kawai muke fuskanta ba — muna ganin wani salo ne na goge makomar ƙasar ta dindindin," in ji wakilin shirin ci-gaba na MƊD a Sudan.
Yaƙi ya jefa fiye da kashi 70 cikin 100 na 'yan ƙasar Sudan cikin talauci, in ji MƊD
[Tohon hoto] Fire da mutum miliyan 21 a Sudan na fuskantar tsananin rashin tabbacin abinci, in MƊD. / Reuters / Reuters
2 awanni baya

Kimanin mutum bakwai cikin 10 a Sudan suna rayuwa cikin talauci a yanzu, a cewar shirin ci-gaba na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) wato UNDP, lamarin da ya kusa ruɓanya halin da ƙasar ke ciki kafin yaƙi ya ɓarke tsakanin soji da dakarun RSF shekara uku da suka gabata.

"Kafin yaƙin, muna ganin kimanin kashi 38 cikin 100 na mutane ne ke rayuwa cikin talauci, kuma a yanzu muna hasashen kimanin kashi 70 cikin 100," in ji wakilin shirin UNPD na ci-gaba na MƊD a Sudan Luca Renda ranar Talata, yayin da hukumar ta fitar da wani sabon rahoto kan talauci da ta fitar daidai da lokacin tunawa da lokacin da yaƙin ya ɓarke.

Alƙaluman da Renda ya yi ishara da su sun dogara ne kan ma’aunin talauci na $4 a ko wace rana, yayin da aka yi imanin cewa aƙalla kashi ɗaya cikin huɗu na mutanen ƙasar suna rayuwa ne kan ƙasa da rabin wannan, in ji shi.

Masu AlakaTRT Afrika - Matsalar yunwa a Sudan: Miliyoyin mutane na cin abinci sau ɗaya a rana

Yanayi ya tsananta a wasu yankunan da lamarin ya fi shafa, ciki har da wasu sassan kudancin Kordofan, wanda a yanzu shi ne muhimmin fagen yaƙin, da kuma North Darfur, inda abin da ya kai kashi 70 zuwa kashi 75 cikin 100 na mutane suke rayuwa cikin rashi, in ji Renda.

‘Goge makomar ƙasar ta dindindidn’

A yanzu cikin shekararsa ta huɗu, yaƙin tsakanin sojin Sudan da kuma rundunar RSF ya kashe dubban mutane da kuma raba fiye da mutum miliyan 11 da gidajensu da kuma tura wasu wurare cikin yunwa da fari.

Masu AlakaTRT Afrika - Matsalar yunwa a Sudan: Miliyoyin mutane na cin abinci sau ɗaya a rana

Masu ba da agaji za su hallara a birnin Berlin ranar Laraba domin wani taro na ƙasa da ƙasa game da rikicin, wanda aka yi domin farfaɗo da tattaunawar zaman lafiya da ke fama da rashin tabbas da kuma tattaro tallafi ga ɗaya daga cikin matsalolin jinƙai na duniya da suka fi tsanani.

"Shekara uku da fara rikicin, ba wata matsala kawai muke fuskanta ba — muna ganin goge makomar ƙasar ta dindindin," in ji Renda .

Mutum miliyan 21 na fuskantar tsannain rashin tabbas na abinci

Rahoton na UNDP ya gano cewa kusan mutum miliyan bakwai ne aka tura cikin tsananin talauci a shekarar 2023 kawai, yayin da matsakaicin kuɗin shiga ya faɗi zuwa matakan da rabon a ga irin su tun shekarun 1992. Matakan tsananin talauci sun fi na shekarun 1980 ƙamari, in ji rahoton.

"Waɗannan alƙaluman ba na tunani ba ne kawai," in ji Renda. "Suna bayyana yanayi na iyalan da aka ɗaiɗaita da yara da ba sa zuwa makaranta da hanyoyi samun kuɗaɗen biyan buƙata da aka rasa da kuma wasu mutane da yiwuwar kyawun makomarsu ke raguwa babu ƙaƙƙautawa."

Fiye da mutum miliyan 21 a Sudan na fuskantar tsananin rashin tabbas na samun abinci, yayin da kashi biyu cikin uku na mutanen ke buƙatar tallafi, in MƊD.

Sai dai kuma masu sharhi ba sa ganin wata alama rage yaƙi sai dai ɗan kaɗan, inda yaƙi ke zafafa a yankin Kordofan da jihar Blue Nile, in ji MƊD.