Fafaroma Leo XIV ya nufi ƙasar tsakiyar Afirka ta Kamaru da wani saƙo na zaman lafiya da kuma tattaunawa da Shugaba Paul Biya, shugaba mai shekara 93 wanda aka tsawaita wa’adin mulkinsa karo na takwas a wani zaɓen da aka musanta sakamakonsa sosai a shekarar da ta gabata.
Fadar Vatican ta ce ana tsammanin ziyarar da Leo zai fara ranar Laraba a Yawunde babban birnin ƙasar ta mayar da hankali kan yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar da ke da arzikin ma’adinai da kuma tattaunawa game da yadda ya dace a yi amfani da ikon siyasa.
Leo na tafiya zuwa Kamaru ne daga Aljeriya, inda ya fara tsayawa a ziyararsa ta ƙasashe huɗu a Afirka.
Shugaba Biya shi ne shugaba mafi yawan shekaru a duniya kuma ya jagoranci ƙasar ta tsakiyar Afirka tun shekarar 1982.
Tsarin tafiya
Leo zai gana da Biya da zaran ya isa fadar shugaban ƙasa a babban birnin ƙasar Yawunde. Kana zai gabatar da jawabi ga hukumomin gwamnatin Kamaru da wakilan ma’aikatan gwamnati da jami’an diflomasiyya kafin ya ziyarci gidan marayu da wasu mata ‘yan zuhudu na ɗarikar katolika, wato nun a harshen Ingilishi, ke jagorantar sa.
Leo na da muhimman taruka biyu a Kamaru, inda mafi muhimmancin cikin su zai kasance wani “taron zaman lafiya a” ranar Alhamis a birnin Bamenda da ke arewa maso yammacin Kamaru, wanda ke fama da tashin hankali .
‘Yanaware daga cikin ‘yan ƙasar masu amfani harshen Ingilishi sun fara neman warewa ne a shekarar 2017, domin ɓallewa daga mafi yawan ƙasar masu amfani da harshen Faransanci domin kafa wata ƙasa mai cin gahin kanta mai amfani da harshen Ingilishi, lamarin da ya janyo tashin hankali .
Rikicin ya kashe fiye da mutum mutum 6,000 tare da raba mutum 600,000 da gidajensu , in ji ƙungiya mai bincike ta International Crisis Group.
Ranar jajibirin isowar Leo , ‘yanawaren sun yi shelar dakatar da yaƙi na kwanaki uku domin ba da damar “tafiya cikin aminci” ga ziyarar Leo.
Gamayyamar ƙungiyoyin ‘yanaware, da ake ce wa Unity Alliance, ta bayyana a wata sanarwar da ta fitar da yammacin Litinin cewa dakatar da faɗan na nuna “muhimmancin addini” na ziyarar wanda zai bai wa fararen hula , da mahajjata da manyan baƙi damar tafiya cikin aminci.
Ɗaya babban taron da Leo zai halarta a Kamaru, inda kashi 29 cikin 1000 na mutanen ƙasar ‘yan ɗarikar Katolika ne , shi ne wani taron ibada ranar Juma’a a birnin Douala, inda ake tsammanin mutum 600,000 su halarta.
Ranar Asabar, Leo zai nufi Angola a mataki na uku na tafiyarsa, wadda za ta ƙarƙare a mako mai zuwa a Equatorial Guinea.










