Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya bayyana cewa tattaunawar da aka yi da Iran ta gaza cim ma matsaya, yana mai ƙari da cewa Amurka ta gabatar da “buƙata ta ƙarshe kuma mafi kyawu” bayan doguwar tattaunawa da aka yi a birnin Islamabad na Pakistan.
Da yake magana bayan shafe kusan sa’o’i 21 ana tattaunawa a babban birnin Pakistan, Vance ya ce har yanzu Amurka tana bai wa Iran lokaci don ta yi la’akari da buƙatun da aka gabatar.
“Mun bar nan da tabbatacciyar buƙata, wata hanyar fahimta wadda ita ce tayinmu na ƙarshe kuma mafi kyawu. Za mu gani ko Iraniyawa za su karɓa,” in ji shi.
Vance ya ce tawagar Iran ta zaɓi rashin karɓar sharuɗɗan Amurka, inda ya ƙara da cewa tattaunawar ba ta riga ta samar da sakamako mai gamsarwa ba.
“Ba mu ga hakan ba tukuna. Muna fatan za mu gani,” in ji shi, yana nufin alƙawari daga Iran na tabbatar da daina ƙera makaman nukiliya.
Ya bayyana cewa babban abin da ke haddasa taƙaddamar shi ne shirin nukiliyar Iran, yana mai jaddada cewa Amurka tana neman tabbaci na dogon lokaci.
“Gaskiyar magana ita ce, muna buƙatar ganin tabbataccen alƙawari cewa ba za su yi makamin nukiliya ba, kuma ba za su nemi kayan aikin da za su ba su damar ƙera makamin cikin sauri ba,” in ji Vance.
Iran ta yi watsi da buƙatu masu ‘yawa’
Iran ta bayyana cewa tattaunawar za ta yi nasara ne kawai idan Amurka ta janye abin da ta kira buƙatu masu “yawa” waɗanda suka “saɓa wa doka.”
Kakakin Ma’aikatar Wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce ci gaban tattaunawar ya dogara ne kan yadda Amurka za ta nuna “gaskiya da niyya mai kyau” sannan ta amince da “haƙƙoƙi da muradun Iran na halal.”
“Nasarar wannan tsari na diflomasiyya ta dogara ne kan gaskiya da niyya mai kyau na ɓangaren da muke adawa da shi, da guje wa buƙatu masu yawa da waɗanda suka saɓa wa doka, da kuma amincewa da haƙƙoƙi da muradun Iran na halal,” in ji shi.
Baghaei ya ƙara da cewa tattaunawar ta ci gaba ba tare da tsayawa ba, inda aka yi musayar saƙonni da rubutattun buƙatu tsakanin ɓangarorin biyu.
Ya ce tattaunawar ta shafi batun Mashigar Hormuz, shirin nukiliyar Iran, biyan diyyar yaƙi, ɗage takunkumai, da kuma “kawo ƙarshen yaƙi baki ɗaya a kan Iran da ma yankin baki ɗaya.”
Haka kuma, Baghaei ya ce Iran ba ta manta da abin da ya kira “yaudarar” Amurka da kuma tarihin saɓa alƙawuran da ta yi a baya ba.










