Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya (NEMA), tare da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta ƙasar sun karɓi ‘yan Nijeriya 179 da suka dawo daga Libya a ƙarƙashin wani shiri na tallafi ga waɗanda ke son komawa ƙasaru na hukumar kula da ‘yan ci-rani ta duniya.
Wata sanarwar da NEMA ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Laraba ta ce jami’anta sun tarbi ‘yan Nijeriya da suka biyo jirgin Al Buraq Airlines ne da misalin ƙarfe 4:15 na yamma ranar Talata a filin jiragen sama na Murtala Muhammed.

Sanarwar ta ce a cikin waɗanda suka dawo ƙasar akwai balagaggu 162, waɗanda suka haɗa da maza 95 da mata 67, da kuma ƙananan yara 9 da kuma jarirai 8.
“Suna dawowa, jami’an hukumar shige da ficen Nijeriya sun musu rajista kuma suka tattara bayansu domin iya gane su wane ne da kuma yadda za a haɗa su da al’ummar ƙasar,” in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ta ce an bai wa waɗanda suka dawo taimako na jinƙai ciki har da abinci da ruwa da kulawa na jami’an kiwon lafiya da kuma taimako na jigilar kayayyakinsu bisa manufar gwamnatin tarayyar ƙasar ta tabbatar da dawowa cikin aminci da mutunci da kuma tausayi.
Kazalika sanarwa ta ce an kuma bai wa waɗanda suka dawo ɗin shawarwari domin tallafa wa mutanen a ƙoƙarinsu na sake haɗewa da al’ummar ƙasar.








