An ji fashe-fashe guda biyu masu ƙarfi da amon harbe-harben bindigogi a kusa da babban sansanin sojin Mali, Kati, a wajen babban birnin Bamako, kuma an jibge sojoji sannan sun rufe hanyoyi a wannan yanki, in ji shaidu.
Ƙarar harbin bindiga ya girgiza wasu gundumomi na wannan ƙasar Afirka ta Yamma a ranar Asabar, ciki har da Kati — yankin da shugaban mulkin soja na ƙasar Janar Assimi Goita ya fito — kamar yadda shaidu da wata majiya daga ɓangaren tsaro suka bayyana wa AFP.
Ba a fayyace abin da ya janyo fashe-fashen ba, kuma babu wata ƙungiya da ta yi iƙirarin ɗaukar alhakin hare-haren.
Ƙasar ta tsakiyar yankin Sahel na fama da hare-hare daga rassan Al-Qaeda da Daesh na Yammacin Afirka. Haka kuma ta jima tana fama da yunƙurin ɓallewa daga masu fafatukar da abzinawa ke jagoranta a arewacin ƙasar.
Gwamnatin da Janar Assimi Goita ke jagoranta ta dogara kan sojojin haya na Rasha don tallafin tsaro, yayin da a farko ta ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da ƙasashen Yamma. A kwanan nan, ta nemi farfaɗo da hulɗa da Amurka.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito a watan Maris cewa Mali da Amurka sun kusa ƙulla wata yarjejeniya wadda za ta ba Washington damar sake amfani da sararin samaniyar ƙasar wajen tashin jiragen sama da jirage marasa matuki don tattara bayanan tsaro a saman sararin samaniyar ƙasar Afirka ta Yamma don tattara bayanai kan kungiyoyin makamai da na ta'addanci.













