| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Tottenham na neman masanin lafiyar tunani ga ‘yanwasanta, don gujewa fadowa daga gasar Firimiya
Sabon kocin Tottenham, Roberto De Zerbi ya gano cewa ƙungiyar na fama da raunin zuciya, inda yake jaddada buƙatar ƙarfafa zuciya.
Tottenham na neman masanin lafiyar tunani ga ‘yanwasanta, don gujewa fadowa daga gasar Firimiya
Tottenham na cikin ƙungiyoyin ƙwallo shida mafi girma a Ingila / Reuters

Tottenham Hotspur ta saka tallan neman sabon masanin lafiyar tunani don warkar da matsalar da ‘yanwasanta ke ciki ta rashin karsashi yayin da suke tararrabin faɗowa daga gasar Firimiya, zuwa ƙaramar gasar Championship ta Ingila.

A halin yanzu Tottenham, wadda ake lissafawa cikin manyan ƙungiyoyi shida na Ingila, tana cikin ƙungiyoyi uku na ƙasan teburin Firimiya.

Dole ne ƙungiyar ta lashe wasanni biyar da suka rage mata a kakar bana, don fatan tasowa sama cikin ƙungiyoyi 17 na saman teburi don kauce wa babban ƙalubalen rikitowa daga Firimiya.

Tun shigowar 2026, Spurs ba ta yi nasara a ko da wasa guda ba, wanda ya janyo mahukunta tunanin cewa rashin karsashi ya shiga zukatan ‘yanwasan har a cikin fili.

Rahotanni na cewa a halin yanzu Tottenham tana neman jami’in da ya ƙware wajen iya ƙara ƙwazo. Hakan na nuna cewa mahukuntan suna ganin kyautata taka ƙwallo kacal ba zai warkar da matsalarsu ba.

Sanarwar neman masanin lafiyar tunanin ta fayyace abubuwan da ake buƙatu wajen masanin, tana cewa, “Muna neman fitaccen masanin tunani, gwanin wajen ƙara ƙwazo don ya shigo tawagarmu ta ƙara ƙwazo”.

Sabon kocin Tottenham, Roberto De Zerbi ya gano cewa ƙungiyar na fama da raunin zuciya, inda yake jaddada buƙatar ƙarfafa zuciya.

Ya faɗa a wasansu na ƙarshe inda suka yi 2-2 da Brighton, "Ina alfahari da ƙwazon su, suna buƙatar nuna ƙarin jajircewa da mayar da hankali kan wasanmu da Wolverhampton, kuma su zo filin atisaye ranar Litinin da murmushi….”