| Hausa
RAYUWA
3 minti karatu
Sirrin lafiyata: Shugaban Uganda Museveni ya ce ya kai kusan shekara 50 bai ci shinkafa ba
Shugaba Yoweri Museveni, mai shekaru 81, ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan ya yi magana game da yadda yake son abincin gida na Afirka, wanda ya ce yana taimakawa wajen ƙara masa ƙarfi da lafiya.
Sirrin lafiyata: Shugaban Uganda Museveni ya ce ya kai kusan shekara 50 bai ci shinkafa ba
Shugaba Yoweri Museveni ya ƙarfafa wa 'yan Uganda gwiwa kan su koma ga cin abincin gida wato na Afirka. / TRT Afrika English

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya bayyana cewa, bai ci shinkafa ba a tsawon kusan shekara 50, lamarin da haifar da ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.

Shugaban ya ce ya daina cin shinkafa tun daga shekarar 1979 bayan da ya dawo daga gudun hijira a Tanzania.

Kafafen yada labarai na cikin gida sun ambato Museveni yana cewa: "Ban ci shinkafa ba tun daga lokacin da na dawo daga Tanzania a shekarar 1979. Ina da abincina: rogo, gero, ayaba, wake, gyada," yayin da yake jawabi a wani taron jam'iyyarsa ta siyasa a gundumar Kyankwanzi da ke yankin Buganda, a ranar 10 ga Afrilu 2026.

To, me yasa shugaban Uganda ba ya son shinkafa a ire-iren cimakarsa?

Abincin Afirka

Shugaban na Uganda mai shekaru 81, ya hau mulki ne a 1986, kuma ya bayyana cewa ya fi son abincin Afirka kamar gero saboda yawan sinadarai masu gina jiki da suke da su sannan suna taimakawa wajen kara masa ƙarfi da kuma lafiya.

Museveni ya kuma bayyana cewa, ba wai kawai kiyaye yanayin cimakarsa yake yi ba.

Yana son ƙarfafa samar da abinci daga cikin gida da kuma rage shigo da shi daga ƙasashen waje domin rage tasirin matsalar abinci a duniya da kuma haɓaka tattalin arzikin gida.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Museveni ke irin wannan tsokaci game da abincin da yake ci ba.

A shekarar 2020, ya ce ba ya cin burodi da shinkafa saboda dukkansu baƙin abinci ne a Afirka, yayin da ake kyautata zaton shinkafa ta samo asali ne daga yankin Asiya.

Ko da yake, ya bayyana cewa abincin da yake ci wanda ba asalin na Afrika ba ne shine dankalin turawa, kuma yana daraja nauyin abincin saboda yana da ƙarancin kalori.

A lokuta da dama Museveni yana yawan ƙarfafa wa 'yan Uganda gwiwa kan su koma ga nauyin abincin gida.

Sai dai, yanayin cin abinci a Uganda da sauran ƙasashen Afirka ya bambanta.

Dafa-duka

Shinkafa, abinci ne da ake ci a kusan kowace ƙasa, inda zamani da kuma yanayin rayuwa suka sa ake sarrafata ta hanyoyi daban-daban, kamar ɗanɗanon dafa-dukar shinkafa na yawan janyo muhawara da gasa tsakanin ƙasasashen Yammacin Afirka kamar Ghana, Nijeriya, Senegal da kuma Sierra Leone.

A Uganda, yawan cin shinkafa yana ƙaruwa da kashi 4 cikin 100, wanda ya zarce tan 300,000 a kowace shekara, a cewar Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya, FAO, a shekarar 2023.

FAO ta ce. a duk shekara buƙatar shinkafa a ƙasashen Yammacin Afirka na ƙaruwa da kusan kashi 6 cikin 100, adadi mafi yawa a abinci da ake ci na yau da kullun.

Sai dai, mafi yawan shinkafar da ake ci a faɗin nahiyar ana shigo wa da ita ne daga ƙasashen waje, galibi daga yankin Asiya, inda gwamnatoci da sauran al’umma ke kashe biliyoyin daloli a kowace shekara don samu.

Yawan dogaro kan shigo da kayayyaki daga ƙasashen waje shi ma yana sa su zama masu rauni ga canjin kasuwa na duniya.

Wasu masu sharhi sun ce wannan shine dalilin da ya sa matsayin Museveni zai iya faɗaɗa muhawarar da ake yi game da tsarin abinci da ayyukan noma a Afirka.